Jaruman Kannywood da ba Yan Nigeria Bane
Kokasan adadin jaruman Kannywood wadanda suka kasance bayan Nigeria bane
A yau munkawo muku jerin Sunayen su dakuma takaitaccen bayani da ya shafesu.
Wasu daga cikinsu kunsan sunayensu dama kasashensu wasu Kuma ba lalle kusansu ba.
Hakan yasa ma aikatan northloaded.com.ng sukai nazari wajen lissafa muku sunayensu dakuma takaitaccen bayani dangane da su.
Jerin jaruman Kannywood wadanda suka kasance bayan Nigeria bane sun hadada.
Hadiza Aliyu Gabon
Kusan kowa yasan hadiza Gabon ba haifaffiyar Kasar Nigeria bace bisa la’akari da sunan Gabon da ake kiranta dashi.
An haifi hadiza Gabon ne a kasar Gabon, Jahar libreville, Mahaifinta yakasance Dan Gabon, mahaifarta Kuma Yar jahar Adamawa dake Kasar Nigeria.
Karanta: Cikakken tarihin hadiza gabon
Safiya Musa
Safiya Musa haifaffiyar kasar Ghana na Daya daga cikin Jaruman Kannywood wadanda ba Yan Nigeria bane.
An haifetane a jahar Accra Dake kasar Ghana sannan acanne tayi Karatunta kamin shigowarta Nigeria.
Karanta: Cikakken Tarihin Safiya Musa (Safiya Ghana)
Diamond zarah
Diamond zarah na cikin jerin jaruman Kannywood wadda ba asalin haifaffun kasar bane Kuma ta samu shahara cikin masana’antar Kannywood.
Diamond zarah Yar asalin kasar niger ne kamin shigowarta masana’antar Fina finan Hausa dake Nigeria
Karanta: Cikakken tarihin diamond zara
Aknan bamenda
Jaruma Aknan bamenda wacce tafito cikin Shirin farin wata wadda adam a Zango yashirya ta kasance asalin yar Garin Bamenda be Dake kasar kamaru (Cameron).
Jarumar na cikin jerin jaruman Kannywood wadda ba asalin haifaffun kasar bane, Jaruma Aknan Bamenda na magana da harshen hausa, fulatanci, dakuma faransanci.
Karanta: Cikakken Tarihin Aknan Bamenda
Rakiya moussa poussi
Ko kuntuna da Jarumar nan data fito tareda Adam A Zango a Shirin Aisha Humaira?
Idan Baku tinaba Nasan kunsanta a video wakokin Hausa da ake sakewa a manhajar YouTube musammman wakokin Hamisu Breaker da Garzali miko.
rakiya moussa poussi takasance haifaffiyar kasan Niger ce Amma a yanzu tananan a Nigeria Saboda harkokin ta na yau da kullum.
Fati Niger
Fati Niger Daya daga cikin mawakan Hausa dasuka shahara suka Kuma samu daukaka da nasarori dadama takasance haifaffiyar kasar niger ne hakannema yasa ake mata laqabi da Fati Niger.
Momy Niger
Momy Niger na Daya cikin jaruman dake taka rawa cikin Shiri Mai dogon zango wadda musbahu Anfara ke shiryawa.
Itama tashigo cikin jerin jaruman Kannywood wadda ba asalin haifaffun kasar Nigeria Bane.
Karanta: CIKAKKEN TARIHIN DADDY HIKIMA
Amina Amal
Jaruma Amal Umar na cikin jerin jaruman Kannywood wadda ba asalin Yan kasar bane.
Takasance asalin yar kasar kamaru dake cikin masana’antar Kannywood
Domin kallon video dangane da Jaruman Kannywood da ba Yan Nigeria Bane kokuma wasu bayanai dasuka danganci masana’antar Kannywood kuziyarci YouTube channel namu a NW Hausa TV.
Kuyi SUBSCRIBE