Tarihin Shatu Garko ( Shatu Garko Biography)

Tarihin Shatu Garko ( Shatu Garko Biography)

Cikakken suna: Shatu Sani Garko

Inkiya: Shatu Garko, Mrs Hijabi, Mrs Beuty Nigeria

Kasa: Nigeria

Jaha: Kano

Gari: Garko local Government

Addini: Islam

Aure: Babu

Shatu ce Tarihin Shatu Garko ( Shatu Garko Biography) ta farko mai hijabi da ta lashe gasar a tarihi kuma wannan ne karo na 44 na gasa
SARAUNIYAR KYAU

WACCECE SHATU GARKO

Shatu sani garko sarauniyar kyau ta Nigeria a shekarar dubu biyu da ashirin da Daya zuwa da biyu 2021-2022 (44th miss Nigeria 2021-2022).

Shatu ce mace ta farko mai hijabi da ta lashe gasar a tarihi kuma wannan ne karo na 44 na gasar wadda ake kira Miss Nigeria a Turanci.

Karanta:

Tarihin Lsvee (Lsvee Biography, Net worth, Songs)

Tarihin Shatu Garko ( Shatu Garko Biography)
Shatu Garko

HAIHUWAR TA

Shatu Garko takasance haifaffiyar Nigeria ce asalin Yar jihar Kano, Garin Garko sannan an haifetane a ranar 23 November 2003 WADDA Izuwa yanzu tanada Shekaru Goma sha Takwas (18).

GASAR SARAUNIYAR KYAU

Sarauniyar Kyau ta Najeriya ta 44, Shatu Garko wacce ta kasance asalin yar Jihar Kano ce ita ta wakilci yankin arewa maso yammacin ƙasar.

Shatu Sani Garko Ta karɓe kambun ne daga hannun Etsanyi Tukura ‘yar Jihar Taraba, wadda ta lashe gasar a karo na 43 a 2019.

A cewar masu shirya gasar, wadda ta yi nasara za ta samu kyautar kuɗi naira miliyan 10, da zama a gidan alfarma na shekara ɗaya, da sabuwar mota, da kuma zama jakadiya ta musamman ga wasu kamfanoni.

NASARORI

Garko na da shekaru 18 a shekarar 2022 Sannan nasarar data samu yajawo maganganu dadama musammman a yankin arewacin Nigeria.

Karanta: Cikakken Tarihin Dezell (Dezell Biography)

Inda mutane dayawa keganin cewa tarbiyarta zai baci ganin duk wadanda suka ci abaya ba mutane babe masu sanya hijabi sannan sukan dauki hotuna dake nuna tsiraci a fili.

Kamfanin kera motocin KIA Dake a kasar China ta sanya shatu matsayin ambassadorn kamfanin na Nigeria Sannan tabata kyautar mota wadda aka kera a Kamfanin.

AURE

Yazuwa yanzu 2022 Shatu Bata da Aure sannan Babu wani saurayi data nunawa duniya shi a matsayin abokin tafiyarta.

Domin Karin bayani dangane da Tarihin Shatu Garko ( Shatu Garko Biography) kokuma wasu jaruman kuziyarci YouTube channel namu a NW Hausa TV

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *