Cikakken Tarihin Safiya Musa (Safiya Ghana)

Cikakken Tarihin Safiya Musa (Safiya Ghana)

Suna: Safiya Yakubu

Inkiya: Safiya Ghana

Aiki: Jaruma

Aure: Babu

GARI: Accra

Kasa: Ghana

Cikakken Tarihin Safiya Musa (Safiya Ghana)
Safiya Ghana tareda momee niger

WACECE SAFIYA YAKUBU

Safiya Yakubu wacce akafi sani da safiya ghana matashiyar jaruma ce a masana’antar fina-finan hausa mai suna “Kannywood” daga yankin Arewacin Najeriya. Kasancewarta sabuwar fuska ba kowane yasanya ko yasaba ganin shirye shiryenta ba saide a farkon Shekarar 2022 ganin fitowarsu tareda fitaccen Jarumin Nan Adam a Zango Yasa tarun jama’a Neman bayani akan Jarumar Wadda hakan yataimaka sosai wajen haskawar taurarinta a ciki dama wajen masana’antar.

Karanta: Cikakken tarihin isah feroskhan Presidor

Haihuwarta

An haifeta a ranar 12 ga watan Yuni, a jihar Accra, dake kasar Ghana. An fi saninta da cikakken sunata Safiya Yakubu Amma ana kiranta da Safiya Ghana kasancewarta Yar kasar.

Safiya Ghana a najeria

Safiya Ghana Ta koma jihar Kano a Najeriya. Bayan ta kammala karatunta inda ta shiga masana’antar fina-finan Hausa, mai suna Kannywood.

Anfara ganin Jarumar ne a vidiyon wakoki wadanda ake sakewa a tashar YouTube inda yafito tareda jarumai dadama Kamarsu Kb international, Garzali Miko dadai sauransu.

Shigarta Masana’antar kannywood

Safiya Yakubu ta shiga masana’antar Kannywood ne a shekarar 2017, tare da taimakon gogaggen jarumin Kannywood, ‘Sadiq Sani Sadiq’, wanda ya yi mata jagora izuwa masana’antar fina-finan Hausa.

Tana da burin zama jaruma tun farko, kamar yadda ta bayyana. Yanzu ta cika burinta.

Daukakarta

Safiya ta samu karbuwa sosai saboda taka-rawar dayayi a fim din “Sadiq-Sanam”, inda tasamu sanuwa sosai a Masana’antar. Hakan ya taimaka sosai fagen aikinta na wasan kwaikwayo a Masana’antar.

A Shekarar 2022 yafito tareda Fitaccen jaruminnan Adam a Zango a vidiyon wakar “Sa’a” dakuma wakar “Alkawari” Wadda Auta Mg Boy ya rera inda aka saki vidiyon a Adam a Zango official YouTube channel.

Yafito tareda jarumi Kb international a wakar da Hamisu Breaker yayi mai suna Dake nake sannan suka hau wakar Zumar Kauna a shekarar 2021

Cikakken Tarihin Safiya Musa (Safiya Ghana)

Tasake fitowa tareda Danta Bashir a wakar Soda Kama Wadda channel din Ayatullahi Take tadauka a Shekarar 2020

A Shekarar 2017 Jarumar yafito a vidiyon wakar Ruhi tareda musbahu Anfara Wadda aka sake a channel din Aka Anfara.

Tafito a vidiyon wakar Nuratu tareda Tykin Mai Gashi Wadda channel din Sarauniya Tv ta haska

Karanta : CIKAKKEN TARIHIN SADIQ SANI SADIQ

Fina finanta

Wannan kyakkyawar jarumar ba ta tsaya nan ba, ta fito a fina-finai da dama kamar su -Sadiq-Sanam
-Bintu, Mai Laya
-Rayuwar macen soja
-Kaddara da sauransu.

Mabiya

Jarumar nada tarun dubunnan mabiya a shafukan sada zumunta inda takeda followers samada dubu tamanin da takwas (88k followers) a Shekarar 2020

AURE

Ya zuwa yanzu Safiya Ghana batada miji Bata Kuma sanarda wani Wadda ta tsayarda wani Wadda ta fadeshi a matsayin saurayinta ba.

Domin samun Karin bayani dangane da Cikakken Tarihin Safiya Musa (Safiya Ghana) ku ziyarci YouTube channel dinmu NwHausa Tv

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *