CIKAKKEN TARIHIN NAFISA ABDULLAHI

Cikakken tarihin nafisa abdullahi

SUNA: nafisa Abdullahi, nafisa sai wata rana

SHEKARU: 23 Jan 1992 (shekaru 30)

AURE: babu

AIKI: Jaruma,producer,daukan hoto, darakta, kasuwanci.

JIHA: Jos, Plateau

KASA: Nigeria.

tarihin nafisa Abdullahi

WACECE NAFISA ABDULLAHI

Nafisat Abdullahi takasance darakta, maishirya fim, mai daukar photo, yar’kasuwa kuma fitacciyar jaruma a masana,antar kannywood. Jarumar wacce tasamu shahara a fadin afrika da sauran kasashen duniya.

HAIHUWAR JARUMAR

Anhaifeta a 23 January 1992 a jos cikin plateau.

Ta fara karatunta a makarantar “Air Force Private School” garin jos inda ta karasa a makarantar “Government Girl Secondary School, Dutse” dake garin Abuja.

Sannan tayi karantunta na Jami’a a makarantantar Jami,ar dake garin jos.
Jarumar takuma karanta ilmin daukar hoto a Jami,ar London a kasar England

FARA FIM

Ta fara fitowa a fim nata na farko me suna (sai wata Rana) a kamfanin (FKD) Wanda yake mallakin ali nuhu a shekarar 2010 tun tana yar shekara 18. Jarumar tafito ne a film din Saiwatarana tareda jarumai irinsu Ali Nuhu, Adam A Zango, Fati Washa dasauransu wadda hakan ya taimaka wajen samun daukakarta da kuma haskakawar tauraron ta.

Karanta Cikakken tarihin baballe hayatu

Sannan Jarumar tayi fim me suna Blood and heyna a shekarar 2012 a mana’antar nollywood tare da Sadiq Sani sadiq, da alinuhu. Tasamu nasarar shiga jerin kyaututtuka sama da shida da shirin. Kuma tasamu nasarar lashe kyautar karramawa ta kwararriyar jaruma daga 9th Africa Movie Academy Awards.

Jarumar tayi shiri dadama a kannywood irinsu Abdulmalik, Ahalul kitab, Gaduhu ga haske daku lamiraj shirinda ya jamata nasarar lashe Gwarzuwar jaruma ashekarar 2013.

Jarumar tasamu nasarori dadama kuma tana daya daga manyan
jarumai Mata a masana’antar ta kannywood wadda kawo yanzu tayi samada fina-finai 50.

Ashekarar 2020 taja ragamar wani shiri mai dogon zango wadda Aminu saira, tareda dan’uwansa Naziru Ahmad dakuma Nazifi Asnanic suka shirya mai suna “Labarina”Tare da jarumai da yawa kamarsu nuhu Abdullahi
maryam waziri Da sauransu shirinda ake haskawa a tashar Arewa24.

HADAKA

Jarumar tayi fim tare da jarumai dadama wasu daga ciki sune kamarsu:

*Adam A zango wanda tsohon saurayintane
*alinuhu
*Sadiq Sani sadiq
*nuhu Abdullahi
*ahmed sadiq
*Ibrahim maishinku

JERIN FINAFINANTA

Tayi fimafinai da dama kamarsu:

-sai wata rana 2010
-Blood and heyna 2012
-ya daga Allah
-madubin dubawa
-toron giwa
-ummi
-yar agadez
-ahalul kitab
-alhini
-baban sadiq
-alhaki kuikuyo
-blood heyna
-Dan marayan zaki
-dare
-cikin waye
-guguwar so
-zango
-laifin dadi
-lamiraj 2013
-madubin dubawa
-baiwar Allah
-labarina 2020

KYAUTAR GIRMAMAWA

Takarfi kyautuka da dama daga kungiyoyi da dama a fadin duniya kamarsu
-city people entertainment award
-Africa movie academy award
-Mtn award
-kannywood award
-afro Hollywood award
-amma award
Da sauransu

Karanta Cikakken tarihin fati shu’uma

Ashekarar 2013 ta karbi kyautar karramawar “Gwarzuwar Jarumar shekara” daga city people entertainment awards da shirinta maisuna “Ya daga Allah”.

Ashekar 2014 tashiga jerin wadanda suka cancanci kyautar karramawa ta “Gwarzuwar shekara” daga city people entertainment awards. Amma batai nasarar lashewa ba.

Ashekarar 2014 ta karbi kyautar karramawar ta “Gwarzuwar jarumar kannywood” daga 1st kannywood awards. Dashirinta maisuna ” Dan marayan zaki”.

Ashekarar 2014 tasake lashe kyautar karramawa ta “Gwarzuwar Jarumar kannywood” daga African movie academy awards da shirinta na “Dan marayan zaki”.

Ashekarar 2016 tashiga jerin wadanda suka cancanci kyautar karramawar ta “Gwarzuwar jaruma” daga city people entertainment awards. Amma batai nasarar lashewa ba.

Ashekarar 2016 ta karbi kyautar karramawar “Gwarzuwar jaruma” daga 2nd kannywood awards.

Kyautar karramawa ta “Gwarzuwar jaruma” daga city people entertainment awards.

AMMA awards ta karramata a matsayin “Gwarzuwar jaruma” a shekarar 2016 a shirinta na da’iman.

Sannan ta kasance jarumar kannywood Mace mafi shahara a fadin duniya

Ta kuma je kasashe da dama kamarsu:
_England
_Dubai
_Indian
_U.S.A
Da sauran kasashen africa

Domin Karin Bayani dangane da cikakken tarihin nafisa abdullahi a YouTube Nw Hausa Tv

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *