Jerin jaruman Kannywood Dake fito wa cikin fina finan Nollywood

Jerin jaruman Kannywood Dake fito wa cikin fina finan Nollywood

Masana’antar Kannywood masana’anta ce da ake shirya Fina finai a harshen hausa dakuma nuna al’adu irin na Hausawa.

Masana’antar Kannywood takasance masana’antace wacce tafi kowace masana’anta tarun masu kallo a yankin Africa ta kudu.

Daga dayan bangare kuwa munada dayar masana’antar Mai cibiya a kudancin Kasar wato masana’antar Nollywood.

Masana’antar Nollywood kuwa sabanin Kannywood tana shirya Fina finai be a harshen Turanci.

Zamu lissafa muku jerin jaruman Kannywood wadanda ke fitowa a dukkannin masana’antun shirya fim na Kannywood dakuma Nollywood.

Jerin jaruman Kannywood Dake fito wa cikin fina finan Nollywood

Ali Nuhu

Jerin jaruman Kannywood Dake fito wa cikin fina finan Nollywood
Ali Nuhu

Ali Nuhu wadda yakasance jarumi ne mai shirya fim Kuma Mai bada Umarni a masana’antar Kannywood na Daya cikin jaruman Kannywood wadda ke fitowa a dukkannin masana’antun shirya fim na Nollywood dakuma Kannywood.

Jarumin wadda akewa laqabi da sarki a masana’antar Kannywood (King of Kannywood) yakasance mutum na farko Daya fara zuwa masana’antar Nollywood, Kazalika yayiwa jarumai dadama sanadin fara fitowa cikin Fina finain Kannywood.

Yafito cikin Fina finain kamarsu:

Banana
Blood and hyena
Island ghost
Confusion
Dear affy
Last man flight to Abuja
Oju kokoro
Dadai sauransu

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN ALI NUHU

Rahama Ibrahim Sadau

Jerin jaruman Kannywood Dake fito wa cikin fina finan Nollywood
Rahama Sadau

Babu shakka zamu iya cewa Rahama ce mace tafarko cikin jaruman Kannywood mata Masu fitowa a Nollywood wacce datafi kowa samun taru lambobin yabo da girmamawa.

Fina finain Rahama Sadau a masana’antar Nollywood sun hada da:

Son of the khaliphet
The other side
Shuga naija TV
If I’m president
Up north
Ajuwaya
Tatu
Zero hour
The accidental spy
Chief Daddy dasauransu.

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN RAHAMA SADAU

Sani Mu’azu

Jerin jaruman Kannywood Dake fito wa cikin fina finan Nollywood
Sani mu’azu

Sani mu’azu na Daya cikin fitattun jaruman Kannywood Dake fitowa a dukkannin masana’antun shirya Fina finain na Kannywood dakuma Nollywood.

Sani mu’azu jarumi ne, Kuma Mai bada Umarni dakuma shirya Fina finai a Kannywood Mafiya yawancin Al’ummar Hausa sun sanshine a shiri Mai dogon zango wadda ake shiryawa a tashar arewa24 Mai suna ” Kwana casa’in”.

Ya yi suna a masana’antar fina-finan Hausa ta Najeriya, kuma ya shafe sama da shekaru 20 yana gogewa a harkar fim da talabijin da rediyo.

Mu’azu yasamu fitowa cikin Nollywood a Fina Finai Kamar haka

1. ”Shuga” (TV Series, 2013),

2 ”Newman Street” (TV Series, 2014),

3 ”Lion Heart” (2018),

4 ”Up North” (2018) , da kuma
5 ”Sarkin Samari” (2018).

Usman Uzee

Jerin jaruman Kannywood Dake fito wa cikin fina finan Nollywood

Na Daya cikin jerin jaruman Kannywood wadda ke fitowa a Fina finain Nollywood wadda ke da cibiya a kudancin Kasar

Usman Ya shirya kuma ya fito a fina-finai da dama kamarsu ;

Oga Abujauja, Maja, Dark Closet, Power of Gobe, Hassana da Hussaina, Har da mijina, Muqabala (Season 1&2), Red Line, Dear Affy, If I am President, Lagos Real Fake Life, Mustapha, Almost Perfect, Least Expected. Maimuna, Sharo, Good citizen among others Dasauransu.

SANI MUSA

Sani Musa Danja na fitowa a shirye shiryen masana’antun Kannywood dakuma Nollywood.

Kusan duk Mai kallon Fina finain Hausa yasan sani Musa Danja domin za’a iya lissafashi cikin manyan jaruman Kannywood Goma.

Sani Danja yakasance mawaki, jarumi, Mai shirya fim, Kuma Mai bada Umarni a masana’antar Kannywood.

Jarumin yafito cikin Fina finain Nollywood dasuka hadada:
Daughter of the River
Gold statue,
Number
Dark closet
How I was raped
Guys must be crazy

Karanta: Cikakken Tarihin Sani Danja

Yakubu Mohammad

Mawaki Kuma jarumi Yakubu Mohammad na Daya daga cikin jerin jaruman Kannywood masu bada nasu gudumawar a masana’antar Nollywood.

Jarumi Yakubu Mohammad yasamu nasarori dadama a dukkannin masana’antu biyun sannan yafito a Fina Finain Nollywood Kamar haka:
Dark closet
Lion heart
Fantastic numbers
4th republic
Shuga naija mtv
Dasauransu

yakubuCikakken Tarihin Yakubu Muhammed-Northernwiki

Amal Umar

CIKAKKEN TARIHIN AMAL UMAR
Jarumar Amal umar

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN AMAL UMAR

Bayan kasancewarta jaruma a masana’antar shirya Fina Finain Kannywood Kazalika Jaruma Amal Umar na fitowa cikin Fina finain Nollywood inda tataka rawa a shinnan Mai dogon zango Mai suna shuga naija mtv dadai sauransu.

Domin Karin bayani dangane da masana’antar Mai cibiya a kudancin Kasar wato masana’antar Nollywood kokuma wasu bayanan Kannywood ku ziyarci YouTube channel namu a NW Hausa TV.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *