Cikakken tarihin sabira gidan badamasi
SUNA: hauwa garba
INKIYA: Sabira gidan badamasi, yar auta
SHEKARU: shekara [40]
AIKI: Jarumar fim, yar kasuwa
AURE: Babu
YARA: Daya [1]
GARI: Kano
KASA: Nigeria
WACECE SABIRA GIDAN BADAMASI
Shahararriya kuma ficecciyar jaruma a masana’antar kannywood hauwa garba wadda akafi Sani da yar auta ko kuma sabira a cikin shirin gidan badamashi
Wadda ake haskawa a gidan TV na arewa 24
Takasance jaruma data jima ana damawa da ita a masana’antar ta kannywood Sannan ta bada gudun mawa da dama a masana’antar duba da yanayin rawar da take takawa
Sannan kuma takasance sohuwar matar marigayi rabilu musa dan ibro
HAIHUWA
Sannan anhaifeta ne a jahar kano karamar hukumar bichi
a shekarar 1982
Sannan tayi karatunta na matakin primary a garin bichi bayan ta gama kuma akayi mata auren fari
KaranĀ Cikakken tarihin tijjani asase
AURE
Sannan jarumar ta taba aure har sau uku Sannan ta haifi yara biyu amma daya ya rasu wadda suka haifa tare da marigayi alhaji rabilu musa dan ibro
FARA FIM
Sannan jarumar hauwa garba wadda akafi sani da yar auta ko kuma sabira gidan badamasi ta fara fitowa a fina finan hausa ne da dadewa tun lokacin ba kolo suke sannan tayi wasa a dabe sosai lokacin ba CD
Sannan fim nata na farko shine
_Sakar karu
DAUKAKA
Sannan daukakarta ta farane tun lokacin da ta fito a wani fim mesuna yan uku tare da
*Jarumi dan auta
Da kuma bita zaizai tare da
*Jarumi falalu a dorayi
JERIN FINA FINAI
Sannan ta fito a fina finai da dama kamarsu
_Yan uku
_Bita zaizai
_sakar karu
Dadai sauransu
Sannan tana daya daga cikin jaruman dasuke haskawa a shirin fim Mai dogon zango gidan badamasi wadda ake haskawa a tashar arewa 24
HADAKA
Sannan ta fito a fina finai da dama tare da jarumai da dama kamarsu
*Dan Auta
*Falalu a dorayi
*nura dan dolo
*Adam A Zango
*Sulaiman boshao
*Mustapha nabraska
*baba ari
Dadai sauransu
KaranĀ Cikakken tarihin Naziru Sarkin Waka
KARIN BAYANI
Sannan kamar yadda ta zayyana ita da kanta ta kirkiro kwalliyarta saboda tun suna wasa adabe take fitowa a shagobabbiya
Sannan ta taba auren marigayi rabilu musa dan ibro kuma sun haihu dashi amma dan ya rasu
Sannan abinda yafi sata farin ciki shine taga kowa yana farin ciki
Sannan abinda yafi sata bakin ciki shine batayi abu ba ace tayi
Sannan kamar yadda ta zayyana akwai yarta wadda ta haifa yanzu haka ana damawa da ita a masana’antar kannywood saidai bata baiyana sunantaba
Sannan daku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube NW HAUWA TV domin samun Karin bayani dangane da cikakken tarihin sabira gidan badamasi