Cikakken tarihin Maryam yahaya
SUNA: Maryam Yahaya
SHEKARU: 17 July 1997 (24 shekara)
AIKI: jarumar fim
AURE: babu
GARI: kano
KASA: Nigeria
WACECE MARYAM YAHAYA
Maryam Yahaya zakwakuriyar matashiyar mace kuma shahararriyar jaruma a masana,antar kannywood wacce ta jajirce ta kuma tsallake siradi da yawa wajen ganin ta cimma burinta na zama jaruma wanda izuwa yanzu tayi nasarar cimmawa. Tafara fitowa ne a Shiri mai suna Taraddadi wadda tayi nasarar shiga “jerin wadanda suka cancanci Kyautar karramawa ta jaruma mai nagarta” daga city people entertainment awards a shekarar 2017.
HAIHUWAR MARYAM YAHAYA
An haifetane a 17 july 1997 a Kano cikin goron dutse. Jarumar tayi karatunta na primary a yelwa sannan tayi makarantar secondary a bokabu barrak dake jahar kano amma har izuwa yanzu bata cigaba da karatuba.
FARA FIM
Jarumar ta fara fitowa a finafinan hausa a 2016 duk dacewa a wanca lokacin tana fitowa ne a matsayin karamar jaruma kuma mai tallafawa jarumai. Finafinan ta na farko sun hada da:
-Taraddadi
-gidan abinci
-tabo
-barauniya
Karanta CIKAKKEN TARIHIN AUTA MG BOY
DAUKAKARTA
Daukakarta ya farane a 2017 tun bayan fitowarta a fim me suna mansoor wadda tafito tare da balkisu shema dakuma umar m shariff. Jarumar tataka rawa sosai wadda hakan yabata damar fitowa a manyan finafinai dataja ragama irinsu:
– Jaruma
– Sareena
– Mujadala
– Jummai ko larai
Dasauransu
JERIN FINA FINAN MARYAM YAHAYA
Jarumar tayi finafinai da dama kamarsu:
-mansoor
-Lamba
-Wutar kara
-Hikima
-tabo
-mijin yarinya
-sareena
-hafeez
-sakanin mu
-barauniya
-Mariyah
-mujadala
-jummai ko larai
-matan zamani
-guguwa
-gidan abinci
-jaruma
Amma mafiya yawan finafinan tayisune a kamfanin shirya fim mesuna (FKD) wanda yake mallakin alinuhu ne
KYAUTAR KARRAMAWA
Maryam Yahaya tasha karbar kyautar karramawa a lokuta da dama a kungiyoyi da yawa a fadin duniya kamarsu
-city people entertainment award
-afrikan actress award da sauransu
Karanta CIKAKKEN TARIHIN SADIQ SANI SADIQ
HADAKA
Kuma tayi fim da jarumai da dama kamarsu
*Adam A zango
*Ali nuhu
*Umar m Sharif
*shamsu Dan, iya
*Abdul m Shareef
*Amal umar
*bilkisu shema
*Maryam booth
Dadai sauransu
FITOWA A BIDIYON WAKOKI
Tafito a vidiyoyi da yawa kamarsu
-hafeez tare da Umar m Sharif
-matan zamani da garzali miko
-jaruma da shamsu dan iya
-mujadala Abdul m Sharif da Umar m Sharif
IYAYE
Ibrahim bello (baba)
Rukayya bello (mama)
KASASHE
Sannan jarumar taje kasashe da dama kamarsu
_Saudia Arabia
_Ghana
_Dubai
_Gambia
_Niger
Dadai sauransu
RASHIN LAFIYA
A wasu lokuta jarumar tayi wani rashin lafiya wanda har yaja hankulan mutane yakoma kanta sannan ya zama sana diyyar dakatar da fitowarta a fim a karshe dai jarumar tace bawani rashin lafiya na daban bane kamar yadda mutane suke dauka zazzabine kawai
Domin karin bayani game da cikakken tarihin Maryam yahaya a YouTube Nw Hausa Tv