Cikakken tarihin fati washa
SUNA: Fatima Abdullahi, Fati Washa.
SHEKARU: 21 February 1993 (shekaru 29)
AURE: babu
AIKI: Jaruma
JIHA: Bauchi
KASA: Nigeria
WACECE FATI WASHA
Fatima abdullahi sananniyar jarumar kannywood wadda akafi sanida fati washa na daya daga cikin jarumai wadanda suka Dade suna taka rawa a masana’antar kannywod jarumar ta shahara a nahirar Africa musamman Africa ta yamma takuma yi fina-finai dadama wadanda suka shahara cikin nahiyar.
HAIHUWARTA
an haife ta ne a ranar 21 ga watan February, ashekarar 1993, a jihar bauchi (shekararta 29)
FARA FIM
Jaruma Fatima Abdullahi wacce aka fi sani da fati washa a wasanun kwaikwayo na Hausa, na masana’antar Kannywood ta fara ra’ayin yin shirine tun tana karama a lokacin da take karanta littattafai. Tasha Gwagwarmaya matuka kafin takawo inda take a yanzu domin tafarane a matsayin mai yin hidima wa jarumai.
Karanta Cikakken tarihin saratu gidado
Fati washa tafara fim tin ba’a matsayin jarumar dake Jan ragamar shiriba. Amma tafito a manyan shiri wadda irinsu “Sai Watarana” tareda manyan jaruma irinsu Adam A Zango, Ali Nuhu Lawan Ahmad dakuma nafisat Abdullahi takuma fito a fina-finai irinsu
-salma bankwana
-mai kyau
-Basaja
-matan gida
Da sauransu
DAUKAKAR FATI WASHA
Jarumar tasamu daukakane tin lokacin da tafara Jan raganar manyan fina-finai kamarsu
-Hindu,
-saudat
-Afra
-balkisu
-abdallah
jarumar ta taka rawarta don ganin ta cimma cikar burinta wadda hakan yataimaka wajen haskakawar tauraronta kuma yasa takara sanuwa a cikin masana’antar dakuma nahiyar Afrika gabadaya.
Jarumar tasha samun yabo dakuma karramawa dadama, yanzu jarumar nadaga cikin manyan manyan jarumai a masana’antar ta kannywood.
Kawo yanzu jarumar tanada mabiya dadama a shafukanta na zumunta na Facebook Instagram dakuma twitter.
KYAUTAR KARRAMAWA
Ashekarar 2019 ta Samu karramawar gwarzuwar jaruma a taron karrama ‘yan Fim da aka gudanar ranar Asabar a birnin London.
Bikin wanda ake kira Afro Hollywood Awards ya shafi karrama jaruman fina-finan harsunan Najeriya guda uku Hausa da Yoruba da Igbo da kuma na Inglishi a sassan kasashen Afirka,
Fati Washa ta lashe kyautar ne saboda rawar da ta taka a Fim din ‘Sadauki.’
JERIN FINA FINAI
_Basaja
_Afra
_Salma bankwana
_Balkisu
_Ya daga Allah 2014
_Yar tasha 2015
_Ana wata ga wata 2015
_Baya da kura 2015
_Fari da baki 2013
_Farida
_Gaba da gabanta 2013
_Hindu 2014
_Hisabi 2017
_Jaraba 2011
_Mai kyau
_Matan gida
_Karfen nasara 2015
_Makahon gida 2013
_Saudat
_Abdallah
_Sai wata rana
Dadai sauransu
Karanta CIKAKKEN TARIHIN AMINU SAIRA
HADAKA
Sannan jarumar tafito a fina finai da dama tare da jarumai da dama kamarsu
*Adam A zango
*Ali nuhu
*Nafisa Abdullahi
*Sadiq sani Sadiq
*Nuhu Abdullahi
*Jamila umar nagudu
*Al’amin buhari
Dadai sauransu
Domin Karin bayani game da cikakken tarihin fati washa a YouTube Nw Hausa Tv