CIKAKKEN TARIHIN MOMEE GOMBE

Cikakken tarihin momee gombe

SUNA: Maimuna Abubakar

INKIYA: Momee Gombe

SHEKARA:
28 June 1997 (25 Shekaru)

AIKI: Jaruma, Yar’Rawa

AURE: Babu

JIHA: Gombe

KASA: Nigeria

tarihin momee gombe

WACECE MOMEE GOMBE?

Maimuna Abubakar wacce akafi sani da Momee Gombe takance Yar’rawace kuma jarumar fim a masana’antar kannywood. jarumar na daya daga cikin jaruman da tauraronsu ke haskawa kuma tabada nata gudumawar ta hanyoyi dadama.

HAIHUWARTA

Jaruma maimuna Abubakar haifaffiyar Jihar Gombe ce Wanda hakanne yasa akeyi mata inkiyada momee Gombe.
An haifeta a 28/June/ 1997. Ta Kuma yi karatunta na primary da secondary a Gombe.

Karanta Cikakken Tarihin Khadija Yobe ( Karima izzarso)

DAUKAKAR MOMEE GOMBE

Jarumar takasance tanada ra’ayin Zama Jaruma tun tana yar’karama amma bata samu cimma hakanba saboda auren datayi dawuri. Bayan fitowarta daga gidan aurene ta shiga harkan fim da taimakon shirya finafinan nan Auwal Mu’azu dakuma fitacce matashin mawakinnan hamisu Breaker.

Tafara sanuwa a video Waka da ake daurawa a manhajar YouTube. Inda jarumar tahau video Waka da jarumai irinsu Adam a Zango, Hamisu Breaker, Garzali Miko, Kabiru Kb International, Musbahu aka anfara dasauransu.

Sannan takara sanuwa a Shirin datayi kamarsu “kishin mata” da “asalin kauna” dakuma rawar data taka a Shiri mai suna “Ango” Tareda fittaccen Jarumin nan Adam A Zango.

Jarumar ta Kara matukar sanuwa a video wakar “Jarumar mata” sabida yaduwa da wakar tayi a yankin Afrika.

KARRAMAWA DA YABO

Maimuna Abubakar ta Ambaci Jarumi Adam a Zango a matsayin Mai Shugabanta Kuma Mai bata shawara Gameda abinda yadace, Takuma ambaci sunayen mutane dadama inda tace sun nada gudumawa Kuma sun taka rawa wajen daukakarta ciki harda Hamisu Breaker, Sunusi Oscar 442, Auwal Mu’azu dakuma Adam a Zango daga karshe Kuma tace “tanada burin Zama Babbar Jaruma a masana’antar ” Kuma “tana da ra’ayin taimakawa marayu da marasa karfi

Momee Gombe kamarde saura Jaruma takasance tanada shafuka a Instagram, Twitter dakuma Facebook dakuma mabiya dadama

FINA FINANTA

-Asalin Kauna
-Zainabu abu
-Ango
-Ba amo
-Dan birni makewayi
-Hanifa
-Kishin Mata
-Mai Maya
-Manyan gobe
-Samanja
-Zainul abideel
Dasauransu.

Karanta CIKAKKEN TARIHIN ALI JITA

HADAKA

Sannan jarumar tafito a fina finai da dama tare da manya da kananun jarumai kamarsu.
*Adam a zango
*Ali nuhu
*Umar m shareef
*Ramadan booth
*Shamsu dan iya
*Sultan abdurrazak
Dadai sauransu

Domin Karin bayani akan cikakken tarihin momee gombe a YouTube Nw Hausa Tv

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *