Cikakken tarihin maryam CTV

Cikakken tarihin maryam CTV

SUNA: Maryam Sulaiman

INKIYA: Maryam CTV

AIKI: Jarumar fim

AURE: Babu

YARA: uku [3]

GARI: jigawa

KASA: Nigeria

tarihin maryam CTV
Maryam CTV da maryam malika

WACECE MARYAM CTV

Maryam Sulaiman wadda akafi Sani da maryam CTV shahararriyar jaruma a masana’antar shirya fina finan hausa na kannywood
Takasance jaruma wacce mafi yawanci take fitowa a masayin uwa sannan tana da kamun kai wadda hakannema yasa manya da kananun jarumai a masana’antar suke girmamata

FARA FIM

Sannan jarumar ta fara fitowa a fina finan masana’antar kannywood ne bayan tabar aiki a gidan TV na CTV kuma ta fara a wani fim mesuna
_Babban gari wadda baba dan azumi wato kamaye ya shirya

DAUKAKA

Saidai duk da dadewar jarumar a masana’antar daukakarta ya farane bayan fitowarta a wani fim mesuna
_uwa tace

Karanta Cikakken Tarihin Aminu Shariff Momo Northernwiki

JERIN FINA FINAI

Sannan tafito a fina finai da dama kamarsu
_babban gari
_uwa tace
_sintacciyar mage
_hayaki
_gwarama

HADAKA

Sannan jarumar maryam Sulaiman wacce akafi sani da maryam CTV tafito a fina finai da dama tare jarumai da dama kamarsu
*Ali nuhu
*Adam A zango
*Sadiq Sani Sadiq
*Isah A isah
*Mai shunku
*Hamud booth
*Maryam booth
*Ramadan booth
*Maryam yahaya
*Maryam babban yaro
*Jamila Umar nagudu
*Hadizan saima
*Saratu gidado
*Hajara usman
*rabiu rikadawa
*tijjani faraga
*Kabiru na kongo
Dadai sauransu

KARATU

Kuma jarumar ta taba fara karatun boko amma batayi nisaba tana aji uku 3 aka cireta akayi Mata aure saidai bayan mutuwar auren ta koma makaranta koyan aikin hannu wadda akewa lakabi da best center wadda bayan kammalashi ne ta fada harkar fim dumu dumu Saidai kafin fara fitowa a fim tadau lokaci mai sawo tana aiki a gidan TV mesuna CTV wadda sunan yayi nasarar binta har masana’antar kannywood

Karanta CIKAKKEN TARIHIN UMMI RAHAB

AURE

Sannan jarumar ta tabayin aure har sau biyu sannan kuma tanada yara uku [3] rayayyu sannan biyu [2] sun rasu idan anhada biyar [5] Kenan

KARIN BAYANI

Sanan kamar yadda ta zayyana sakaninta da matasan masu tasowa a masana’antar kannywood ba komai sai girmamawa da ganin mutuncin juna

Sannan ta samo inkiyar CTV ne ta dalilin aiki da ta tabayi a CTV

Sannan jarumar ta fito a fina finai sama da Dari da ashirin a masana’antar kannywwod

Sannan daku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube NW HAUSA TV domin samun karin bayani dangane da cikakken tarihin maryam CTV

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *