CIKAKKEN TARIHIN AUTA MG BOY

Cikakken tarihin auta mg boy

SUNA: Auta Mg boy

CIKAKKEN SUNA:
Abdulrahman Muhammad garba,

SHEKARU:
1 January 1993 (28 Shekaru)

AIKI: Waka, jarumi

AURE: babu

JIHA: kaduna

KASA: Nigeria

Cikakken tarihin auta mg boy
Mg Boy

WANENE AUTA MG BOY

Abdurrahman Muhammad garba,
Wanda akafi sani da (Auta Mg boy)
Shahararren matashin mawakin Hausa wanda ya samu shahara a fadin nigeria da wasu kasashen afrika, kasancewar manyan jarumai irinsu Adam a zango, Kb international, Momee Gombe, Rakiya Moussa, Ummi rahab dasauransu suna hawa wakarsa.

Mawakin yana kuma hawa bidiyon wasu daga cikin wakokinsa domin shine dakansa ya hau wakarsa ta ” Baba ayimini Aure ” wacce tayi silar daguwarsa.

HAIHUWA

Anhaifi shi a shekarar 1993 a kaduna cikin Zaria Sannan yayi karatunsa acikin Zaria.

 FARA WAKAR AUTA MG BOY

Awani hira da akayi dashi ya baiyana cewa shiya kasance me ra,ayin jin wakokin turawa tun yana karami hakan yasa bayan ya girma yaji ra,ayin yin waka da hausa domin kara inganta yarensa dakuma samun damar fadakarwa.

Acewar Mawaki auta mg boy shi Mai sauraron wakokin Umar m Shareef ne hakan Yasa yaji ra’ayin yafara wakoki da salon Umar din.

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN HAFSAT IDRISS

SAMUN DAUKAKAR AUTA MG BOY

Mawakin yasamu Daukaka dakuma shaharane a wakarsa dayayi na “Baba ayi mini aure da Wakarsa ta ” zuciya” da Adam a Zango yahau tare jaruma Momee Gombe Wadda hakan yakarawa jarumin masoya.

Cikin Wakokinsa dasuka yi suna akwai Wakarsa ta “labarina” wadda Momee Gombe tare da Abdul m Shareef suka hau dakuma Videon Wakarsa ta so jani wadda yafito tareda Rakiya Moussa da Real cousin.

A farkon shekarar 2021 mawakin yakara samun Daukaka a Shiri mai dogon zango mesuna ” Farin Wata” da Adam a zango yakeyi a manhajarsa ta YouTube kasancewar shine yayi mafiya yawancin wakokin cikin shirin.

Cikakken tarihin auta mg boy
Auta Mg

HADAKA

Sannan yayi waka tareda *Umar m Shareef, *Adam a zango dasauransu

WAKOKIN AUTA MG BOY

Mawakin yayi wakoki da yawa kamarsu
-yanzuma aka fara
-Baba ayimin aure
-daga ke
-Garin so 2022
-nashiga so
-tintibe
-kina zuciyata 2020
-labarina 2020
-zuciya 2020
-maryama
-masoyiya
Dasauransu

   BIDIYON WAKOKI

-Baba ayi min aure 2020
-Sonki 2021
-Ke nakeso 2021
-Lamarinso 2022
-Kece dai 2022
-Duniyar so 2022
Dadai ssuransu

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN HAMISU BREAKER

Kalli wannan videon Domin Karin bayani dangane da cikakken tarihin auta mg boy a YouTube namu Nw Hausa Tv

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *