Cikakken Tarihin Lilin Baba

Cikakken Tarihin Lilin Baba

Suna: Shu’aibu Ahmed Abbas

Aiki: Waka, Jarumi, Mai rikodin waka

Kamfani: north-East record

Shekaru: 02/02/1992

Karatu: diploma

Aure: Babu

Cikakken Tarihin Lilin Baba
Lilin baba tareda Dan soja

WANENE LILIN BABA

Shu’aibu Ahmed Abbas Wadda akafi sani da lilin baba yakasance mawaki, marubucin waka, Mai rikodin waka, jarumin fim sannan Kuma dan’kasuwa.

Shine mamallakin kamfanin north East record Wadda a ciki yake rera duk wakokinsa sannan kamfanin ita tadau nauyin shirya Fina finai masu dogon zango masu suna wuff dakuma sirrin zuci.

Lilin baba yakarbi kyaututtuka dadama a harkansata waka ciki hadda City People Entertainment Awards a 2018 inda ta karramashi a matsayin Arewa Most Promising Music Act of the Year. Sannan ya lashe kyautar Arewa Best RnB Music Act of the Year 2019 a City People Entertainment Awards.

HAIHUWARSA

Lili yakasance haifaffen garin gwoza ne Wadda ke jihar Borno. An haifeshi a watan janairu Shekarar alib dari Tara da casa’in da biyu 2/02/1992. Iyayensa sune Ahamad Abba (mahaifi), sannan Binta Ahmad (mahaifiya).

karanta: CIKAKKEN TARIHIN KHADIJA BUKAR ABBA IBRAHIM

KARATU

Lilin baba yayi karatunsa na madatakin primary da secondary dama makaranatar gaba da secondary wato diploma duk a jihar Borno kafin mawakin yashigo masana’antar Kannywood domin fara harkarsa ta waka.

FARAWA

Mawakin yafara ne da harkarsa ta wakokin R&B tin a shekarar 2016 Wadda kawo yanxu yayi wakoki sama da 100.

Sannan za’a iya cewa Yana daga cikin manya manyan wakan R&B na arewacin Nigeria kasancewar yadda yasamu karbuwa dakuma tarun masoya cikin kankanin lokaci.

Saide duk da jimawarsa a masana’antar Kannywood jarumin baitaba fito a kowace fim ba saide Shekarar 2020, inda yafito a wani fim da Abubakar Bashir Maishadda ya shirya maisuna Hauwa kulu kafin daga baya yafara shirya nashi fim din Mai dogon zango Mai taken “Wuff”.

DAUKAKA

Daukakarsa yafarane tin bayar wakarsa mai suna Aisha dayayi shekarata 2018, wakar tasamu karbu sannan takasance itace silar sanuwarsa domin itace wakarsa tafarko dayayi video mata video yafara sakewa a YouTube channel dinsa.

Daga bisani sukai wata waka tareda Ado gwanja Mai suna girgiza baya, dakuma Zance yakare.

Kana daga bisani sukai waka tareda Umar m Shariff maisuna Bazama dakuma Tsaya dakuma wakar dasukai da Umar m Shariff da Mr bangis dashi lilin baba mai suna sarki goma.

JERIN WAKOKINSA

Aisha 2017
Girgiza baya ft Ado Gwanja 2018
Baya Baya 2018
Nida Kune 2018
Asha ruwa 2018
Zance yakare ft Ado gwanja 2018
Swagun karyane
Bazama ft Umar m Shariff Bounce
Take 2018
Tsaya ft Umar M Shariff and Rahama Sadau 2018
Inda Inda 2019
Sarki Goma ft UMAR M Shariff and Mr Bangis
Ranar Aure ft Dan umma
Best Hausa culture wedding ft Dan umma
Inda Dadi ft Maryam Ab Yola 2020
Swagu karyane ft Adam a Zango and Abdul tynking Mai Gashi

Duniya
Xee
Suri
Voom
Taka Rawa 2020

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN DJ AB

Farida ft Ali JITA 2021
Kolo 2021
Duniyar 2021
GARI ya waye 2021
Zata ft Soja boy 2021
Ahaiyye ft Umar m shareef 2021
Tsaya ft Umar m Shariff 2021
Overload ft Adam A Zango 2021
Takarawa 2021
Yar mama 2021
Jinja 2021
Bawata 2021
Voom 2021
Gimbiya 2021
Ahaiyye ft Umar m Shariff
Abaya
Dan Mama 2021
Gangar rawa 2021
Sautin Rawa 2021
Suri 2021
Zara ft Soja Boy
Rigar so staring Ummi Rahab
Mata 2022
Ruwan Madara 2022
A wamba Domitina ft lilin baba 2022
Yarinya 2022
Matso 2022, Sai ke 2022
Zo Gani 2022
Inna Ganki 2022
So 2022
Zauna 2022

Cikakken Tarihin Lilin Baba
Lilin Baba

AURE

Yazuwa yanzu (2022) mawakin Bashir da mata saide yasha yin posting na Jarumar nan wacce suke Shirin wuff da ita “Ummi rahab” a Instagram nasa inda yake kiranta da masoyiyarsa.

MABIYA

Jarumin Kuma mawakin kamardae duk wani tauraro yanada tarun magoya baya a kafafun sada zumunta inda yakeda samada mutum samada dubu dari uku da tamanin (380k) followers a Instagram a Shekarar dubu biyu da ashirin da biyu 2022.

Domin Karin bayani dangane da Cikakken Tarihin Lilin Baba zaku iya ziyartarmu a shafin YouTube channel dinmu a NwHausa TV.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *