Cikakken tarihin rabiu daushe
SUNA: Rabiu Ibrahim
INKIYA: Daushe
MATA: Daya
YARA: Uku
AIKI: Jarumi, dan wasan barkwanci, darakta, kuma furodusa, dan kasuwa.
GARI: Kano
KASA: Nigeria
WANENE RABIU IBRAHIM DAUSHE
Shahararren kuma ficecce gogagge a harkar fim sannan daya daga cikin wadanda sukafi dadewa a masana,antar shirya fina_finan hausa na kannywood
Rabiu Ibrahim daushe wadda akafi Sani da daushe
FARA FIM
Daushe ya fara fitowa a fina finan barkwan tun a shekarar 1999 a bangaren chamama kafin daga bisani ya fara fitowa a fina finan kannywood sannan ya fara fitowane a wani fim mesuna
_Aljannar dan auta da
_amalala
JERIN FINA FINAI
Sannan yafito a fina finai da dama kamarsu
_Alkalin kauye
_Asibitin mahaukata
_Aljannar dan auta
_Andamali
_Dan auta amalala
_garbati
_hanyar kano
_hawayena
_ibro ba sulhu
_jamila mai wasa da jura
_jam baki
_sohon lawya
_Karfen nadara
_Kayi nayi
Karanta CIKAKKEN TARIHIN KB INTERNATIONAL
Sannan yafito a
_Gidan badamasi
Shiri mai dogon zango wadda ake haskawa a tashar arewa24
Sannan ya fito a
_karema da ranarsa fim mai dogon zango
HADAKA
Sannan yafito tare da jarumai da dama a fina finai da dama kamarsu
*Adam a zango
*Ali nuhu
*Hadiza gabon
*Ayatullahi tage
*Ibro
*Dan auta
*naburaska
*Dan dolo
*Hauwa waraka
Dadai sauransu
IYALI
Sannan rabiu ibrahim daushe yanada mata daya da yara uku
1)bashir rabiu Ibrahim daushe
2)Ibrahim rabiu Ibrahim daushe
3)Fatima rabiu Ibrahim daushe.
KARIN BAYANI
Sannan rabiu ibrahim daushe bayan kasancewarsa jarumi amasana,antar kannywood ya kasance dankasuwa, tela kuma yana saida yadi
Sannan yakasance na hannun daman marigayi rabilu musa dan ibro
Sannan yakasance dan fari a gidansu sannan yana da kanne sha daya
Sannan shi da kansa yasawa kansa suna daushe a wani wasan barkwanci dasukaje yi a jahar bauchi
HAIHUWA
Sannan anhaifeshi ne a jahar kano karamar hukumar wudil dake jahar kano a Nigeria
Karanta CIKAKKEN TARIHIN FATI WASHA
KARATU
Sannan yayi karatunsa na matakin primary da secondary duk a jahar kano
sannan kafin ya fara fitowa a fim yakasance malamin a wani islamiya mesuna nurul huda sannan kuma ya taba koyarwa a wani primary a cikin garin wudil inda ya karantar da yaren hausa
Sannan daku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube NW HAUSA TV domin Samun karin bayani dangane da cikakken tarihin rabiu daushe