Cikakken tarihin naziru Sarkin waka
SUNA: Naziru M Ahmed
INKIYA: Naziru, sarkin waka
SHEKARU: 4 September 1986
AIKI: Mawaki, Marubucin, darakta
MATA: Biyu
YARA: Biyar
GARI: Kano
KASA: Nigeria
WANENE NAZIRU M AHMED
Naziru m ahmad wadda akafi sanida Sarkin waka, kokuma Naziru yakasance Fasihin mawakine, marubuci, makadi, Kuma basaraken mawaka wadda yake bada gudumawa ta hanyoyi dadama Domin cigaban yaren Hausa da al’adun Hausa dakuma al’ummar hausa harma da ita kanta manana’antar kannywood.
Karanta CIKAKKEN TARIHIN ADAM A ZANGO
HAIHUWARSA
An haifeshi a ranar 4 gawatan September a shekarar 1986 a jihar kano sannan yayi karatunsa kuma ya girma duk a jihar.
FARA WAKA
Acewarsa yafara ra’ayin wakane tin a yarintarsa alokacin sunada abinyin kida (wato piano ) a gida wadda sukan hau wakokin mawakan wancan zamanin irinsu musbahu m ahmed wadda yakasance dan,uwansane da kuma yakubu Mohammed da muddassir kasim inda zasuyita rerawa domin nishadi.
Sannan Mawakin wadda yakasance yafiyin wakokin al’adun Hausa da kuma masarautu Kana yasamu Radin sarauta ne daga masarautar kano a shekarar 2018 matsayin sarkin wakan sarkin kano.
MASANA’ANTAR KANNYWOOD
Naziru yashigo masana’antar kannywood ne a matsayin maiyin editing daga bisani yafara waka.
Yafara wakane a shirin da yayansa mal aminu saira ya bada umarni mai suna “Musnadi” wadda wakar tasamu karbuwa sosai a ciki dama wajen masana’antar kuma tasamu yabo a wajen manya kuma shahararrun mawaka na wancan lokacin hadda mawaki musbahu m ahmed wadda shima yasa muryarsa a cikin Wakokinsa a masana’antar kannywood.
Kawo yanzu yayi waqoqin fim sama da talatin da biyar 35 cikinsu hadda mati da lado, hanyar kano, wani gari, gangar jikinta na Aura dasauransu.
KWAREWA
Baza’ace Mawakin bai kware a harkar wakokin fina finai ba to amma zamu iya cewa Naziru m ahmad yafi KWAREWA a harkar wakar sarauta dakuma na salon gargajiya domin kuwa tabbas a wannan fagen babu kamarsa har ila yau.
Mawakin wadda daga baya yafara wakokin masarautu yasamu tarun nasarori da tarun dukiyoyi dakuma dumbin masoya
KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN RAHAMA SADAU
WAKOKIN MASARAUTU
Wakokinsa na fagen masarautu sun hadada
“Mata kudau turame” “Sabon sarki” “Sunusi lamido” “Ado bayero
Sunusi na biyu” da sauransu.
Karanta:
IYALI
Mawaki Naziru m ahmad yanada mata 2 dayara 5 cikinsu hadda yarsa mace mai suna “islama”
Sannan yakasance kanin fasihin mai bada umarninnan mal aminu saira
Sannan kuma kanin mawaki musbahu m ahmed
JERIN WAKOKINSA
Kawo yanzu jerin wakokin sa sun haura Dari biyu (200) ciki hadda
_Ashe shayi
_Abdallah
_Abdulhalim
_Ado Bayero
_Ahmad Musa
_Dan Giya
_Dallatun Zazzau
_Ghazali Maitama da Farida
_Gangar Jikinta Na Aura
_Ba Mutum Bane
_Dan sahu
_Hanyar Kano
_Hadiza
_I Love U Forever and Ever
_Jarman Wudil
_Kanin Miji
_Kuliyan Zazzau
_Lamido
_Mai Abu Bakwai _Sardaunan Gora
_Mata Kudau Turame
_Matar Jami’a
_Mati Da Lado
_Muhammad Rahman
_Murnar Sabon Sarki
_Musa Jidda
_Na’iman Da’iman
_Sabon Sarki
_Sardaunan Samari
_Sarkin Das
_Soyayya
_Sultan Biyamin
_Sunusi Lamido
_Umar Turawa
_Umaru Ahmad
_Usman Zannuraini _Musa Jidda
_Wani Gari
_Yata Fadimatu
Da sauransusauransu
KYAUTAR GIRMAMAWA
kana mawakin naziru m ahmed yasamu kyautukan girmamawa da dama kamarsu
•best kannywood singer a shekarar 2013
Da sauransu
Sannan yasha karban kayutuka da yawa daga hannun mutane kamarsu kyautar motoci, da kudi, da gidaje, da sauransu
Sannan daku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube mesuna NW HAUSA TV dangane da cikakken tarihin naziru sarkin waka