CIKAKKEN TARIHIN ADAM A ZANGO

Cikakken tarihin adam a zango

SUNA: Adam A Zango, Usher, Prince Zango

Sponsored Links

SHEKARU: October 01 1985 (47) a 2022

AIYUKA : kida, waka, rawa, jarumi, darakta, kuma produsa

MATA: Safiya Adam Chalawa

YARA:  7 bakwai

JIHA: Kaduna

KASA: Nigeria

Cikakken tarihin adam a zango
Prince Zango

WANENE ADAM A ZANGO

Adam a zango mamallakin white house family kuma jarumine a masana’antar kannywood dake arewacin nigeria Wanda akeyiwa lakabi da usher, dakuma prince zango. Yakasance jarumi, marubuci, maibada umarni, Dan rawa, kuma mawaki wadda yayi fice a cikin kasar da kuma wajen kasar. Kadan Daga cikin fina finansa dasukayi fice akwai : basaja, gwaska, hubbi, nass, nidake mundace, Hindu, Abdul mallik dadai sauransu

HAIHUWAR ADAM A ZANGO

An haifi Adam a zango a karamar hukumar zango kataf dake jihar Kaduna na nigeria a October 01 1985. Wadda yakasance Dane ga hajiya yelwa Abdullahi dakuma Mallam Abdullahi.

Daukakar Adam a zango
Kida (music composer)

Adam Abdullahi zango yafara ra’ayin harkar kidane tin yana makarantar secondary ta laranto dake garin plateau a jihar jos.

Bayan kammalar makarantarsa ta secondary baici gabada karatuba sakamakon rashin Wanda zaidauki nauyinsa izuwa matakin karatu nagaba. Wanda a dalilin hakanne yasamu cikakkaiya dama ta cika mafarkinsa nason zama makidi, mawaki kuma jarumin film.
Adam a zango ya bar garin jos zuwa kaduna domin cika mafarkinsa inda yafara da kida wadda ita yafi kwarewa a wancan lokacin. A harkarsa da kida yayi aiki da manya dakuma kananan mawaka na wancan lokacin kamarsu Adamu Hassan nagudu, yakubu mohammed, abubakar sani dadai sauransu.

Bayan samun daukaka a harkarsa ta kidane usher ya shirya wa kansa shiri Wanda yafara fitowa a ciki mai suna “sirfani” ganin wannan shiri da zango yayi yasa jarumi Ali nuhu ya daukoshi yashirya masa film mesuna “fil’azal” inda film din yasamu karbuwa kuma tasashi sanuwa a matsayin jarumi na masana antar kannywood
Kawo yanzu jarumin yayi finafinai sama da 100 kuma yayi aiki da manyan jaruman kannywood kamar su Ali nuhu, Sadeeq Sani Sadeeq, ibro dasauransu

Karanta CIKAKKEN TARIHIN AUTA MG BOY

DAUKAKARSA A HARKAR WAKA

Albulm na Adam zango nafarko itace Bahaushiya albulm me dauke da wakoki 7 album din yasamu karbuwa sosai wacce tasa yayi fice a harkarsa ta waka saide jarumin a yashiga gida kaso a dalilin album dinnasa ta Bahaushiya. Bayan album da Bahaushiya yayi wakoki kamarsu oyoyo, kuka kurciya, ban mutuba dadai sauransu.
Kawo yanzu mawakin yayi wakoki dadama dasuka shafi hip hop, wakar sarauta, R&b dakuma wakar siyasa

MATA DA YARA

A shekarar 2022 Adam zango yanada mata daya Sofia Adam challawa dakuma yara bakwai cikinsu harda mawaki haidar zango. Sofia ba itace matarsa tafariba yakasance ya auri wasu matan kafin ita ciki harda fitacciyar jarumarnan Maryam Ab yola.

Cikakken tarihin adam a zango

KYAUTAR KARRAMAWA DAKUMA YABO

Adam a zango na daya daga cikin jiga jigan yan wasa dakuma shirya fina finai a kannywood. Yakasance daya daga cikin yanwasa wadanda tauraronsu yake haskawa Wanda kuma burin duk wata karamar jaruma ko jarumine yin film dashi. Sannan jarumin yana samun yabo daga dayawa cikin abokan akinsa kadan daga ciki akwai:

nura m inuwa “wadda yakasance mawaki kuma mashiryin film a wakarsa ya yabi zango inda yake cewa “nafada Adam a zango Garkuwatace” hakan na tabbatarda muhimmancin jaruminne a wajen abokin aikinsa nura m inuwa”.

umma shehu “ko cewa tayi Adam ya taka babban rawa wajen haskawarta cikin masana’antar”

Mashiryin shiri, mai bada umarni kuma Dan wasa falalu dorayi kuwa cewa yayi “zango mutumne mai raha kuma mundin kahadu dashi saika sake bukatar haduwa dashi”

Shiko Dan wasa Isah feroz Khan hoton Adam ne a profile nashi na Instagram wadda hakan ke matukar nuna kaunar dayakeyiwa jarumin

Jaruma ummi rahab kuwa sawa tayi a profile nata na Instagram “zango is my Gud father”
Hakan nanuna irin son datakeyiwa jarumin Wanda yasa take kiransa da baba

Awani hira da arewa24 tayida jaruma Aisha aliyu tsamiya tanuna cewa zango ne kusan jaruminda tafison yin film dashi a masana’antar ta kannywood

Dangane da cikakken tarihin adam a zango a YouTube NW HAUSA TV

KYAUTAR KARRAMAWA

Jarumin ya lashe kautar karramawa dayawa a masana’antar ta kannywood yakasance shine mai yawan kyauta karramawa na biyu a masana’antar bayan jarumi Ali nuhu

Ashekara ta 2015 ya kasance cikin jerin wadanda suka cancanci kyauta karramawa har sau goma 11 da film dinshi mai suna Hindu inda yayi nasarar lashe kyaututtuka 6 cikin 11

Yasamu kyautar karramawa daga wazobiya Fm tayi a shekarar 2016 a matsayin jarumin da kware a masana’antar (excellence in the industry)

Jarumin yasamu award daga abalak association

A London yalashe kyautar karramawa da akayi wa African movies

A film nashi mai suna sa’insa a ashekarar 2014 wadda ya fito da jaruma umma shehu tayi nasarar lashe kyautar karramawa ta jarumar datafi kowacce a ashekarar (best actress)

Karanta CIKAKKEN TARIHIN NURA M INUWA

KARIN BAYANI

A shekara ta 2019 zango ya bada gufumawar 47 million domin tallafawa karatun marayu wadda ya Gabatar a fadar sarkin zazzau shehu Idriss
A march 2021 yanada mabiya 278k a YouTube, 1.5 million mabiya a Instagram, 170.5k a twitter, 294,056k a Facebook

JERIN FINA FINANSA

2002
-Albashi
2003
-Gwamnati
-Gwanaye
2008
-Dijangala
2009
-Artabu
2010
-Balaraba
-Ga duhu ga haske
-Laifin dadi
-Sai wata rana
2011
-Adamsy, addini ko al’ada
-adon gari
-ahalil kitab,
-alkawari na, babban yaro -mutallab, Rabin jiki
-ummi da adnan, yar
-agadez, zarar bunu
2012
-Baban sadiq
-Hubbi
-Nageria da Niger
-Rai dai
-Shahuda
-Walijam
2013
-Andamali
-Basaja
-Dutsen gulbi
-Gaba da gabanta
-Nass
-Nidake mundace
-Soyayyar Facebook
-Wata rayuwa
2014
-Bayan rai
-Hindu
-Kaddara ko fansa
-Kama da wane
-Soyayya da shakuwa
-Zinat
2015
-Dare
-Mata ko ya
-Mazan fama
2016
-Gwaska
-Jamila
2017
-Hisabi
-Rumana
-Zulumi
2018
-Dangin miji
-Gudun mutuwa
-Habib
-Ta’addanci
-Umar faruk
2019
-Matatace shaida
-Ruwa a jallo
-Dare daya
-Hisabi
2020
-Burin raina series
2021
-Farin wata series

JERIN FINA-FINANSA DA BA A TABBATAR DA SHEKARUN YINSUBA

_ango da amarya
_Aska Tara
_Auren tagwaye
_Bita zai zai
_Dajin so
_Dan almajiri
_Duniya budurwar wawa
_Farar saka
_Fataken dare
_Ga fili ga mai doki
_Gambiza
_Gamda katar
_Hadizalo
_Ijaabah
_Kare jini
_Kolo
_kundin tsari
_Larai
_Madugu
_Masu aji
_Matsayin so
_Mazan fama
_Mukaddari
_Murmushin alkawari
_Nai maka rana
_Namamajo
_Nusaiba
_Rai a kwalba
_Rawar gani
_Rintsin kauna
_Ruwan ido
_Ruwan jakara
_Salma
_So
_Tarkon kauna
_Tsangaya
_Ya salam
_Zanen dutse
_Zatona
_Zo muzauna

tarihin adam a zango

JERIN WAKOKIN ADAM A ZANGO

-Adon gari
-Aisha
-Alalo alalo
-Allah mai aradu
-Azanto (tare da MR bangis)
-Bahaushiya
-Bakarya
-Ban mutuba
-Binta juju
-Balo balo
-Buje
-Dawo kanon dabo
-Dorina
-Duniya zaman marina
-Duniya
-Duniya rawar wawa
-Fatima
-Galala
-Gambara
-Garin kaduna
-Girgiza
-Gumbar dutse
-Innaga dama
-Kaduna
-Komai daga Allah me
-Mamaye
-Mai dama dama
-Mai gari
-Mai laya
-Makiyana
-Masoyan zango
-Lelewa bahaushiya
-Oyo yo
-Paparazi
-Sabada
-Salima
-Sawa
-Shahuda
-Soyayya
-Tarbiya
-Yar gata
-Wazobiya

HADAKA

Jarumi Adam a zango ya fito a Fina-finai da dama tare da manya da kananun jarumai a masana,antar kannywood harma da wajenta gasunayen wasu daga cikinsu kamar haka
*Jarumi Ali nuhu
*Marigayi s nuhu
*Isah feroshkhan
*Sadiq sani sadiq
*Nafisa Abdullahi
*Jamila umar nagudu
*Tumba gwaska
*Maryam babban yaro dadai sauransu

Domin Karin bayani dangane da cikakken tarihin adam a zango a YouTube Nw Hausa Tv

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *