CIKAKKEN TARIHIN UMMI RAHAB

Cikakken tarihin ummi rahab

SUNA: Rahab salim, ummi rahab

SHEKARU: 2004

AIKI: jarumar fim

AURE: Babu

GARI: Kaduna

KASA: Nigeria

Cikakken tarihin ummi rahab
Ummi rahab

WACECE UMMI RAHAB

Rahab salim wacce akafi sani da ummi rahab fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fana-finai na Hausa wato kannywood

HAIHUWA

An haifi jarumar ne a shekarar dubu biyu da hudu (2004) a cikin garin Kaduna inda tayi karunta na matakin primary dakuma matakin gabada primary
Wato secondary school cikin garin Kaduna sai dai har izuwa yanzu jarumar bata cigaba da karatunta na gaba da secondary ba

FARA FITOWA A FIM

Rahab salim takasance daya daga cikin jarumai dasuka fara shiri a kananan shekaru a cikin masana’anta ta kannywood
Jarumar tasamu karbuwa da kuma sanuwane a shirinta na fari wacce akaiwa laqabi da “Kinzamo Takwara Ummi”
Ummi Rahab tasamu nasarar fitowa a shiri tareda manyar jarumai kamarsu Adam a Zango, Jamila Umar Nagudu, Hadiza Mohammed dadai sauransu

 

Cikakken tarihin ummi rahab
Rahab

DAINA FITOWA A FIM

kana shekarun da suka gabata
Jarumar ta dakatar dayin shiri na ‘yan wasu shekaru sabida cigabada karatunta Saide dawowarta masana’antar a shekarar 2020 yayi matikar Jan hankalin Al’umma inda tasamu daruruwan masoya a shafukanta na Instagram

Karanta CIKAKKEN TARIHIN ABUBAKAR BASHIR MAISHADDA

sannan
Jarumar taja hankalin al’umma ne da wasu hotunanta data wallafa a shekarar 2020 wadanda suke Nuna cikarta shekara 18 da haihuwa Sannan take taya kanta murnar kammala karatunta na matakin secondary

Kana
A farkon shekarar 2021 tafito a shiri me dogon Zango (wato series movie) me suna “Farin Wata” Tareda
*Jarumi Adam a Zango, *Jaruma aknan bamenda
*Jarumi abdul Babulaye dadai sauransu

Bayaga shiri a masana’antar kannywood Ummi Rahab tasha fitowa a vidiyon wakoki tareda mawaka da dama ciki hadda *Adam a Zango, *Sammani AA
*Lilin baba
dadai sauransu

Wadda hakan ya kara taimakawa haskakawar taurarinta

HADAKA

Sannan jarumar tafito a Fina-finai da dama tare da jarumai da dama a masana,antar kannywood kamarsu
*Jarumi adam a zango
*Jarumi kuma mawaki wato lilin baba
*Jaruma Azima gidan badamasi
*Jarumi Abdul m shareef
*Jaruma hadiza Mohammad
*Jaruma jamila umar nagudu
Dadai sauransu

Karin bayani dangane da cikakken tarihin ummi rahab a YouTube Nw Hausa Tv

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *