Cikakken Tarihin Aminu Shariff Momo Northernwiki

Cikakken tarihin aminu Shariff momo

SUNA: Aminu shareef

INKIYA: Momo

SHEKARA: 17 February 1977

MATAKIN KARATU: degree

AIKI: Jarumi, daraka, furodusa,marubuci, Mai gabatarda shirye shirye a tashar arewa 24

MATA: Daya

YARA: uku

GARI: Kano

KASA: Nigeria

Cikakken tarihin aminu Shariff momo
Aminu Shariff momo

WANENE AMINU SHARIFF (MOMO)

Jarumi Aminu Shariff wadda akafi sani da momo ya kasance sanannen jarumi a masana,antar shirya fina-finan hausa na kannywood dake garin Kano a Nigeria da kuma sharhin fina-finai a tashar arewa 24

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN ADAM A ZANGO

HAIHUWARSA

Anhaifi jarumin ne a shekarar alib 1977 a anguwar kwale dake Kano a Nigeria.

KARATUNSA

Sannan jarumin yayi karatunsa na primary da secondary a garin Kano.

Sannan yayi karatunsa na jami’a a makarantar Bayero University kano (BUK kano) agarin Kano inda ya karanta political science.

IYALI

Kana jarumin aminu shariff ko kuma momo yakasance yana da mata daya 1 da yara uku 3 biyu daga ciki mazane daya Kuma mace.

Sunayen yaransa Muhammed aminu sharif, da safiyya aminu Sharif, da Aliyu aminu sharif

FARA FIM

Yafara harkan film a masana’antar shirya fina-finan hausa na kannywood ne a shekara ta 1996 amma daukakarsa tafarane tun bayan fitowar a wani shiri mesuna “duniyar sama”

Bayaga haka a shekarar 2015 yafara aikin a tashar tv na Arewa 24 inda yayi fice musamman a bangaren sharhin fina-finai Arewa 24 kasancewarsa me gabatar da sharhin fina-finan

JERIN FINA-FINAI

Jarumi aminu Shariff yayi Fina finai da dama a tarihin rayuwarsa Wanda hakan yayi sanadiyar sanuwarsa a kasar Nigeria dama wasu kasashen afrika
Fina-finan sun hada da
•Kalan dangi
•Ruwan dare
•Duniyar sama
•Tuwon sama
•Dan bala
•Takaddama
•Tuwon tulu
•Guguwa
•Kishiya ko yar’uwa
•Abu naka
•Ukuba
•Kauna
•Acuci maza
•Ana wata ga wata
•Gidan farko
•Kayar ruwa
•Rumana
Dadai sauransu

Cikakken tarihin aminu Shariff momo
Momo

HADAKA

Sannan yafito tare da jarumai da dama a masana,antar kamarsu
*Alinuhu
*Adam A zango
*Jamila nagudu
*Fati washa
*Sadiq sani sadiq
*Baballe hayatu
Dadai sauransu

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN ADO GWANJA

KYAUTAR GIRMAMAWA

Kana Aminu Shariff momo yasha karban kyautar girmamawa da dama a tarihin rayuwarsa ganin yadda jarumin yakeda basira da gwazo sosai a masana’antar ta kannywood kamarsu

• Arewa film award (best actor)

• Gamji award (best actor)

• Afro-Hollywood award (best actor on hausa category)

• Kano state censorship award (best actor)

• City people entertainment (best actor)
Da dai sauransu

Zaku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube mesuna NW HAUSA TV dangane da cikakken tarihin aminu shariff momo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *