CIKAKKEN TARIHIN HALIMA ATETE

Cikakken tarihin halima atete

SUNA: Halima Yusuf Atete, Halima Atete

SHEKARU: 31

AIKI: jaruma, me shirya fim

AURE: Babu

GARI: Borno

KASA: Nigeria

Cikakken tarihin halima atete
Atete

WACECE HALIMA ATETE

Halima Yusuf Atete wacce akafi Sani da Halima Atete tana daya daga manyan jaruman kannywood wadanda sukayi fice dakuma samun nasarori dadama a mana’antar kannywood. Halima Atete takasance Jaruma, kuma me shirya fim a mana’antar. Jarumar tafi kwarewa a rawarda take takawa na Muguwa kokuma mafadaciya a cikin fim rawar da jarumai irinsu Aina’u Ade dakuma Saratu gidado suma suke takawa a masana’antar.

HAIHUWARTA

Anhaiheta a 26 November 1998 a Borno sannan takuma Girma a cikin jihar. Tayi makarantar primary a makarantar primari na maigari, tayi matakin gaba da primary a makarantar “Yerwa government day secondary school” sannan ta Samu Samar shiga diploma inda takaranci zama alkali da sanin dokokin kasa.

Karanta CIKAKKEN TARIHIN UMMI RAHAB

DAUKAKA

Jarumar ta shiga mana’antar kannywood a shekarar 2012. Tayi finafinai samada 160 cikin harda Kona gari, Dakin amarya, Ashabul kahfi, Ba’asi soyayya da shakuwa dasauransu.
Sannan tashirya finafinai dadama irinsu “Asalina” “Uwar Gulma”
dadai sauransu

KYAUTAR KARRAMAWA

A shekarar 2013 ta lashe kyautar karramawa ta Gwarzuwar sabuwar Jaruma saga City people entertainment awards

A shekarar 2014 ta lashe kyautar karramawa ta “Kwararriyar me tallafawa Jaruma” daga city people entertainment awards

Africa’s voice ta saka Jarumar cikin jerin wadanda suka cancanci zama “Gwarzuwar Jaruma”.

2017 tayi nasarar lashe kyautar karramawa ta ” Gwarzuwar Jaruma ” saga city people entertainment awards

Sannan a 2018 ta lashe kyautar karramawa ta “fuskar kannywood” saga city people entertainment awards.

Cikakken tarihin halima atete
Jaruma Atete

FINA FINANTA

-Alkalin kauye
-Asalina
-Ashabul kahfi
-Ba’asi
-Bikin yar Gata
-Bani bake
-Dakin Amarya
-kona gari
-Kurman kallo
-Mai dalilin aure
-Matar jami’a
-mu’amalat
-soyayya da shakuwa
-Wata hudu
-Labarina
dasauransu.

Karanta CIKAKKEN TARIHIN ADO GWANJA

HADAKA

Sannan jarumar tafito a fina finai da dama tare da jarumai da dama kamarsu
*Jarumi adam a zango
*Jarumi ali nuhu
*Jarumi Sadiq Sani sadiq
*Jaruma Aisha aliyu tsamiya
*Jaruma jamila nagudu
*Jaruma nafisa Abdullahi
*Jarumi nuhu Abdullahi
Dadai sauransu

domin Karin bayani

Cikakken tarihin Halima Atete a YouTube Nw Hausa Tv

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *