CIKAKKEN TARIHIN HAFSAT IDRISS

Cikakken tarihin Hafsat idriss

SUNA: Hafsat Ahmad Idriss, Barauniya

SHEKARU : 1987 (34)

AIKI: Yar Kasuwa,
Jaruma, me shirya fim

YARA: Hudu

JIKA: Daya

JIHA: Ogun

KASA: Nigeria

Cikakken tarihin Hafsat idriss
Hafsat idriss

WACECE HAFSAT IDRISS BARAUNIYA

Hafsat ahmad Idriss takasance jaruma a masana’antar kannywood wace akafi sani da Barauniya.

Jaruma Hafsat suna Barauniya ne a shirin ta na farko mai taken “Barauniya” shirin da tafito tareda jarumi Ali Nuhu dakuma Jamila Umar Nagudu.

KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN FALALU A DORAYI

HAIHUWAR HAFSAT IDRISS

an haifi ta ne a ranar 14 ga watan julin a shekarar alib 1987 a gairn shagamu dake jihar ogun. Inda kuma acan tayi karatunta.

Tin kafin shigar jarumar harkar film takasance ita yar kasuwace, takan zo daga oshogbo zuwa kano wadda a sanadin hakanne jarumar taji ra’ayin shiga harkar fim domin bada nata gudumawar.

DAUKAKARTA

Tayi shirinta na farko a kannywood a shekarar 2016 da Shiri mai suna “Barauniya” sannan tayi “makaryaci”. kawo yanzu tauraruwar tana daga cikin shahararrun jarumai mata a masana’antar kannywood.

Jarumar tafito a cikin wani Shiri mai dogon zango na tashar arewa24 wadda Naziru Ahmad, Nazifi Asnanic Dakuma Aminu Saira suka shirya mai suna “Labarina” Ashekarar 2020

Sannn tayi Shiri tare da manyan jaruman kannywood irinsu
*Jarumi Ali Nuhu,
*Jarumi Adam a Zango,
*Jarumi Sani Musa Danja,
*Jarumi Sadeeq sani sadeeq
*Jaruma nafisat abdullahi
dadai sauransu.

ta mallaki kamfanin samar da finafinai mai suna “Ramlat Investment” a shekarar 2018.

Cikakken tarihin Hafsat idriss

KYAUTAR KARRAMAWA

Hafsat idiriss ta samu kyaututtuka da yabo dadama cikin harkar fina-finan Hausa.

Ashekarar 2017 city people entertainment awards ta sa Hafsat Idriss cikin jerin wadanda suka cancanci Kyautar “jaruma mafi yawan Yan wasan kwaikwayo”

2018 tasamu nasarar lashe kyautar karramawa ta “Gwarzuwar jaruma” daga city people entertainment awards.

Kazalika Ashekarar 2019 Jarumar tasake lashe kyautar karramawa ta ” Gwarzuwar jaruma” akaro na biyu daga city people entertainment awards.

Kana a shekarar 2019 Jarumar ta lashe kyautar karramawa ta ” fuskar kannywood” daga city people entertainment awards.

AURE

Hafsat idriss wadda akafi sani da barauniya takasance bata da aure na sawon lokaci tun bayan rabuwarta da mijinta na farko amma tayi sabon aure 18/02/2022.

JERIN FINA-FINAI

Hafsat ta fitu a cikin fina finai da yawa kamarsu:
-Barauniya 2016
-Makaryaci 2016
-Abdallah
-Daban ganshi ba
-Dan almajiri
-Mace mai hannun maza
-Maimunatu
-Matar mamman
-Haske biyu
-Igiyar zato
-Risala
-Rumana
-Wazir
-Tafaru takare 2017
-Dan kurma
-kawayen amarya
-Namijin kishi
-Wacece sarauniya
-Wata ruga
-Yar fim
-Zan rayu dake 2018
-AlQibla
-Ana Dara ga dare yayi
-Dr surayya
-Mata da miji 2020
-Labarina fim medogon zango

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN HAMISU BREAKER

Kalli wannan videon domain karin bayani dangane da cikakken tarihin hafsat idriss a YouTube Nw Hausa Tv

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *