CIKAKKEN TARIHIN ALI JITA

Cikakken tarihin Ali jita

SUNA: Ali Jita

Sponsored Links

CIKAKKEN SUNA:
Isah Ali Jibrin

SHEKARA: 37

AIKI: mawaki, me rubuta waka, mebada umarni, me shirya film.

Mata: Daya 1

YARA: Biyar 5

JIHA: kano

KASA: Nigeria

 

Cikakken tarihin Ali jita
Ali isa jita awajen taro a

WANENE ALI ISAH JITA

Cikakken sunansa yakasance isah ali jibrin Ana masa lagabi da Ali jita a fannin waka, ana kuma kiran shi da mai jita ko Ali isah jita sunanshi na yanka shine Ali isah jibrin ya kasance mawakin Hausa na zamani marubucin waka kuma mai rerawa, mai bada umarni a shirin Hausa na kannywood kuma me shirya fim.

HAIHUWARSA

An haifi Ali jita a shekarar 1983 watan juli ranar 15, a jihar kano cikin garin Gyadi Gyadi. Mawakin ya tashi a shagari quarters a karamar hukumar kumbotso, a garin Gyadi Gyadi, daga bisani suka koma Lagos sabida canjin wajen kasuwanci da mahaifinsa yayi, Bayannan Kuma suka sake Komawa Abuja. sunan mahaifinsa alhaji salisu jibrin kibiya wadda ya kasance mahauci ne, mahaifiyar sa kuma Hajiya ummul_khairi.

MATAKIN KARATU

Ali jita ya fara karatun a noziri a shagari quaters yayi karatun firamari da sakandari a “Victoria Ireland” dake Lagos a cikin wani barikin sojoji mai suna “bonikam barrac”. ya karasa karatun sa na sakandiri ne a abuja. Sannan yayi makarantun matakin diplomansa a federal college of education a garin kano inda ya karanta public administration.

Karanta CIKAKKEN TARIHIN LAWAN AHMED

FARA WAKA

Ali jita ya fara harkan waka tin yana dan
shekara 16, lokacin yana makarantan islamiya a Lagos. Yafara yin waka a lokacin yana makarantar collegi a kano amma a wancan lokaci yakan taba wakarce kadan kadan haka ya cigaba da waka har yazuwa inda yake a yanzu. Ali kasance mutum ne mai saukin kai kuma me sanyayyar murya mutum ne kuma mai yawan murmushi.

IYALAN ALI ISAH JITA

Ali jita yana da aure harda yara biyar (5).
-Usman (Affan)
-Aliyu (Ramadam)
-Ahmad (Farid)
– Zainab (Hidda)
-Aisha (Afra)

Cikakken tarihin Ali jita
Ali jita

SAMUN DAUKAKARSA

ALI jita yayi watawaka mai suna love wakar ta lashe lambar girma na jadawalin wakokin da suka fi kowanne a shekaran, a inda wakan tazo na biyu, kamar yanda BBC Hausa suka dauko rahoto ALI jita yayi amfani da salan lngausa wajen rubuta wakan da kuma rerawa. A shekaran 2019, yayi bidiyon waka sa mai suna arewa angel tare da jaruma Rahama sadau. Sannan yayi bidiyon waka mai suna love tare da Hadiza Gabon Yakuma fito tareda jaruma fati Mohammad a wakarsa ta fati.

WAKOKIN ALI JITA

Yawancin wakokin Ali jita ana saka su a masana’antar fim ta kannywood, Amman wasu daga cikin albom din shi kuma an sayar dasu ne a wajen kannywood, yasha yin waka ne tare da shahararren mawaki nazifi asnanic da kuma fati nijar a matsayin abokan arziki. Harwa yau, shahararren mawakin yayi waka tare da nazir m Ahmad mai suna mama, sannan yayi waka tare da Umar m shareef mai suna kano a shekaran 2018 mawakin yayi waka tareda mawaka dayawa na arewaci dama kudancin kasar.

Karanta CIKAKKEN TARIHIN ZEE PRETTY

LAMBAR GIRMA

Ali jita ya samu lamba girmamawa a fannin waka dadama.

JERIN WAKOKIN ALI ISAH JITA

-Murmushin alkaware
-tambura
-Zaman gida
-Buje remix
-Uwar gida
-Labarin jita remix
-Rayuwa
-Chan changi
-Ga amarya ga ango
-remix
-So sinadari remix
-Rabbna
-Daniya
-Watan azumi
-Farar diya
-Arewa angel
-Mamana
-Tarkon kauna
-Gimiyar mata
-Buri uku
-Yar lele
-Duniya
-Halimatu Sadiya
-Asha ruwa
-Jawabi
-Yara yara
-Kece
-Love
-Indo
-Aure
dadai sauransu.

Domin Karin bayani dangane da cikakken tarihin Ali jita a YouTube Nw Hausa Tv

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *