Cikakken tarihin Zee pretty
SUNA: zulaihat ibrahim
INKIYA: Zee pretty, Z pretty
SHEKARU: 1997
AIKI: jaruma
AURE babu
MATKIN KARATU: NCE
GARI : kebbi
KASA :Nigeriya
WACECE ZEE PRETTY
Zulaihat Ibrahim wacce akafi sani da Zee Pretty na daya daga cikin jarumai a masana’anatar shirya fina finan Hausa wacce akafi sanida kannywood.
Jarumar Nada kwarewa fagen aikinta sannan ta samu kwarewa a fagen rawa dakuma fina finan barkwanci.
HAIHUWARTA
An haifi zulaihat Ibrahim a shekarar alib dubu daya da Dari Tara da chasa’in da bakwai (1997) cikin garin Tuba karamar hukumar Dankuwa a jihar Kebbi dake Nigeria.
KARATUNTA
Jarumar wacce akafi sani da Zee Pretty tayi Karatunta na matakin primary da secondary a jihar kebbi, daga bisani ta samu nasarar zuwa makarantar federal college of education dake jihar sokoto domin cigaba da karatunta na matakin gaba da secondary (Nce).
Bayan kammalawarta ne tasamu nasarar wucewa izuwa makarantar jami’ar Ahmadu bello dake garin Zaria domin karatunta na matakin degree.
Sannan Acewar jarumar zulaihat Ibrahim tana da matukar ra’ayin zama jaruma a masana’antar shirya film tun tana yar karama kasancewar tanada sha’awar kallon shirye shiryen fina finan Hausa wadda hakanne yabata damar Shiga masana’anatar domin bada nata gudummawar
FARA FIM
Kafin kaiwa ga fara shiri a masana’antar kannywood Zpreety tafara ne da wasan Barkwanci da kuma taka rawa a videon waka wadda ake daurawa a manhajar YouTube.
Karanta CIKAKKEN TARIHIN HAFSAT IDRISS
Sannan Jarumar tafito a videon rawa tareda mawaka dadama wadanda suka hadada Garzali Miko, Auta mg boy, Adam a zango dasauransu.
DAUKAKARTA
Duk dacewa ba wani dadewa tayi a masana’antar ba kamin haduwarta da jarumi Adam a zango amma tabbas haduwarta dashi yataka rawa matuka wajen Haskawar taurarinta domin zpreety tafara samun daukakane a wakar vidiyo wadda Adam a zango yafito da ita mai suna
BABBAN YARO ganin yadda ta taka rawa a wakarne yasa tasamu Karin tarun mabiya dakuma masoya a shafukanta na sada zumunta.
Jarumar ta burge jarumi Adam a zango wadda harya ambaceta da suna “my favourite actress” wato jarumar dake matukar burgeshi hakan yasa yayita fitowa da ita cikin vidiyoyin wakokin daban daban kuma na mawaka dayawa.
Fina finan Zpreety a masana’antar kannywood
JERIN FINA-FINAI
Fina finanta a masana’antar kannywood sun hadada
Shirin makullin zuciya tareda jarumi Adam a zango dakuma abdulrazak sultan
Burin raina shiri mai dogon zango tareda jarumi Adam a zango dakuma isah feroz khan
Gidan badamasi shiri mai dogon Wanda falalu a daurayi ya shiryawa kuma ake haskawa a tashar arewa24 Dasauransu
JERIN BIDIYOYIN WAKOKI
sun hada da
Kama da juna tareda *jarumi Adam a zango ashekarar 2021
Nayarda dake tareda *jarumi Garzali miko a shekarar 2020
Annabi saide kai (wakar bege) ashekarar 2020
Ruwan Zuma tareda *jarumi Adam a zango ashekarar 2020
Abokiyar rayuwa tareda *jarumi Adam a zango ashekarar 2021
Makullin zuciya tareda *jarumi Adam a zango ashekarar 2020
Wakar Babban yaro tareda *jarumi Adam a zango ashekarar 2019
Dadai sauransu
KARIN BAYANI
Bayaga harkar fim jarumar takasance daya daga cikin jarumai kuma yan kasuwa dake cikin masana’antar ta kannywood
Kawo yanzu jarumar batada Aure sannan babu Wanda ta ambata a matsayin wadda tatsayar zata aura amma tace tabbas tanada shirin yin aure nanda Dan wani lokaci kadan
HADAKA
sannan tafito a fina finai da dama tare da jarumai da dama kamarsu
*Jarumi adam a zango
*Jaruma Fati washe *Jarumi falalu a dorayi *Jaruma azima gidan badamasi
Dadai sauransu
Daku iya samun Karin bayani dangane da cikakken tarihin zee pretty a YouTube NW HAUSA TV