TARIHIN LAWAN AHMED ( Umar Hashim Izzar so)

TARIHIN LAWAN AHMED ( Umar Hashim Izzar so)

SUNA: Lawan Yahaya Ahmed

SHEKARU: 13 March 1982

MATA : daya

YARA: 3 Maza biyu Mace daya

AIKI: Jarumi, Mai shirya film, mamallakin Bakori tv.

JIHA: Katsina

KASA: Nigeria

TARIHIN LAWAN AHMED ( Umar Hashim Izzar so)
Lawan Ahmad tareda Balkisu shema

WANENE LAWAN AHMED

Lawan Jarumine kuma mashiryi shiri a masana’antar kannywood a karkashin kamfanin FKD film production Wanda Jarumi Ali nuhu yake jagoranta.

Yana na daya daga cikin jaruman dasuka Dade suna taka rawar gani a masana’antar ta kannywood

Sannan jarumin yakasance daya daga cikin yan takarar kujerar house of assembly a karamar hukumar bakori dake jihar katsina
Sannan jarumin kamar yadda ya zayyana ashirye yake sab domin fafatawa da duk wani abokin hamayyarsa ashekarar 2023 yayinda postarsa ta karade shafukan sada zumunta kana yakasance dan jam,iyyar APC

HAIHUWARSA, KARATUNSA

An haifi Jarumi lawan yahaya Ahmed a 13, march, 1982 a garin BAKORI dake jihar katsina. Jarumin yayi makarantarsa ta primary a Nadabo primary school Bakori (1987 zuwa 1993) Bayan kammala makarantarsa ta primary ne kuma ya Shiga makarantar Government day secondary school Bakori inda yayi karatunsa na junior (1994 zuwa 1997) dagananne kuma ya tsallaka izuwa Government Day secondary school Sharada(1997 zuwa 2000) domin kammala matakin secondary school.

Jarumin yaci gabada karatunsa na gabada secondary school a makarantar Federal college of education kano saga (2002 zuwa 2004) daga nanne kuma jarumin ya samu admission a makarantar Yusuf Maitama Sule University.

TARIHIN LAWAN AHMED ( Umar Hashim Izzar so)

DAUKAKAR JARUMIN

lawan yahaya Ahmed ya shiga masana’antar kannywood a matsayin Jarumi a shekarar 1999 inda yafara fitowa a cikin shirinsa nafarko maisuna *siradi* Jarumin yasamu nasarar fitowa a manyan fina finai na cikin masana’antar Kamarsu
-Sai watarana tareda *Jarumi Adam a zango, *Jarumi Ali Nuhu
dakuma
*Jaruma Nafisat Abdullahi

Sannan
yakara samun daukakane a shirinsa mai dogon zango mai suna Izzar so daga kamafanin Bakori Tv a manhajar YouTube. Shirin izzar so yasa Jarumin yakara sanuwa ga wadanda basusanshiba Dakuma wadandama suka sanshi.

Karanta CIKAKKEN TARIHIN YUSUF SASEEN

IYALAN LAWAN AHMED

Yanada mata daya dakuma yara uku. Daga ciki biyu mazane dayar kuma mace wacce itace karamar su.

JERIN FINA-FINANSA

-Abinda kayi,
-Bakace,
-Bani ba ce
-Haske
-Hauwa kulu
-kalamu waheed
-muradin raina
-ni da kai da shi
– kolo, maya
-sai watarana
-sansani
-shanya
-sharhi
-sayin daka
-Taraliya
-wasila 2010
-zuma, dadai sauransa

KYAUTAR KARRAMAWA

A shekarar 2014 yasamu nasarar fitowa cikin jerin Mtn Award na “sabbin jarumai masu hazaka”

A shekarar 2016 Mtn Award ta karramashi a matsayin wanda “yafi kowar Tallafawa jarumai” (Best supporting actor)

Akuma shekarar 2017 yasamu karramawa daga katsina Hero Award matsayin Wanda yafi kowa shahara

Shekarar 2018 yakara Samun karramawa daga *City film Award da film nashi na ‘Da’iman’ a matsayin wanda ” yafi kowar Tallafawa jarumai” (Best supporting actor)

Ya samu nasarar shiga jerin Jarumai dasukafi kowa a 2019 (Best Actor) daga “Afro Hollywood Award London” da film nashi maisuna zan rayu dake

A shekarar 2019 yasake samu nasarar fitowa cikin jerin jarumai dasukafi kowa (best actor) daga Amma Award 2019.

HADAKA

sannan jarumin ya fito a Fina-finai da dama tare jarumai da dama kamarsu
*Jarumi Ali nuhu
*Jarumi Adam A Zango
*Jarumi Salisu s fulani
*Jaruma Nafisat Abdullahi
*Jaruma khadija yobe
*Jaruma Aisha najamu
*Jarumi Adam A adam
Dadai sauransu

Domin Karin bayani dangane da TARIHIN LAWAN AHMED ( Umar Hashim Izzar so)

TARIHIN LAWAN AHMED ( Umar Hashim Izzar so)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *