Cikakken tarihin Ali nuhu
SUNA: Ali Nuhu, Sarki Ali, yaya Ali
SHEKARU: 15 March 1974 (48)
MATA: [1] Maimuna Garba Abdulkadir
YARA: [2] Fatima Ali Nuhu, Ahmed Ali Nuhu
AIKI: Jarumi, darakta, produsa, mai koyarda rawa, Dan kasuwa.
JIHA: Maiduguri, Borno
KASA: Nigeria
WANENE ALI NUHU
Ali Nuhu Jarumine Wadda yayi fice kuma ya taka rawa wajen cimma Daukakar sa. Jarumi Ali Nuhu Yayi fice A Nigeria dama sauran kasashen Ketare Sakamakon fitowa dayake a dukka bangarori biyu na Masana’antar Fina finan Dake kasar wato Nollywood da kuma kannywood. Ali Nuhu dai Jarumine, maibada umarnine, mashiryin shirine, marubucine kuma mai koyarda rawane.
Jarumin yafara shiri tin a shekarar 1999 har izuwa yanzu Inda jarumin ya fito a fina finai samada 200
HAIHUWARSA
An haifeshi a jihar Maiduguri Borno state dake arewa maso Gabashirn Nigeria. Ashekarar 15/03/1794. Mahaifinshi Nuhu paloma asalin dan garin Balanga ne dake jihar Gombe state, mahaifiyarsa Fatima Karderam Digema yar garin Bama ce dake jihad Borno.
KARATUNSA
Ali Nuhu ya Girma a kano inda yayi primary da secondary school a cikin garin. Dagananne yasamu damar shiga jami’a a garin Jos inda ya karanci geography.
Bayan yagama yatafi bautar kasa a garin Ibadan dake jihar oyo. Sannan Jarumin ya hallarci makarantar jami’a dake kudancin California a America inda yayi karatu a bangaren shirya fim
Karanta CIKAKKEN TARIHIN AMAL UMAR
DAUKAKARSA
Ali yafara harkan film a shekarar 1999 da shirinsa nafarko maisuna ‘Abin sirri ne’ amma jarumin ya samu karbuwa da kuma sanuwane a wajen jama’a da shirinsa mai suna *sangaya* kawo yanzu jarumin yafito a Fina finai sama da Dari biyu a dukka masana’antu dake Nigeria kadan daga ciki sune: Madubin dubawa, jarumin maza, last fight to abuja, confusion Na Wa, dasauransu. Jarumin yataka rawa a shiri mai dogon zango dayayi fice a arewacin kasar “izzar so” inda yafito a matsayin matawalle. Ali Nuhu yayi waka tareda jarumai dadama cikin kannywood kamarsu Adam a zango, sadeeq sani sadeeq, lawan Ahmad, baballe hayatu, Abba el Mustapha, jamila Umar nagudu, hadiza aliyu gabon, Fatima washa, balkisu shema, rahama sadau, maryam yahaya dasauransu
Ashekarar 2019 Jarumin yayi murnar cikarsa shekara 20 a masana’antar film.
A Neman iliminsa na harkan fina finai Jarumin yaje kasar India domin daukar horo a makarantar ” Asian school of media studies” a Noida, dake New Delhi a India.
Sannan Jarumin wadda akeyiwa laqabida Sarki a masana’antar kannywood na daya daga cikin jaruman dake kawo cigaba a masana’antar ta kannywood
FINA FINAN ALI NUHU A KANNYWOOD
-mujadala
-charbin kwai
-jinin jikina
-madubin dubawa
-mansoor
-matan gida
-nasibi
-gida da waje
-matan aure
-toron giwa
-ali zaki
-adamsy
-wani hanin
-wasila
-mai farin jini
-halwa
-andamali
-gidan kiso
-gani gaka
-Hauwa kulu
-zainabu abu
-fati
Dadai sauransu
Kuziyarcemu a shafinmu na YouTube domin samun Karin bayani dangane da cikakken tarihin Ali nuhu NW HAUSA TV
FINA FINANSA A NOLLYWOOD
-Banana
-Blood and henna
-Island ghost
-confusion
-Dear affy
-Last man fight to abuja
-Ojukokoro
Dadai sauranu
SERIES FIM
-Alaqa
-izzar so
-Burin masoyi
-Muqabala
Da sauransu
HADAKA
Sannan jarumin yafito a fina finai da dama tare da jarumai da dama kamarsu
*Adam a zango
*nafisa Abdullahi
*mai shunku
*Sadiq Sani Sadiq
*jamila umar nagudu
*baballe hayatu
*rabiu rikadawa
*rahama Hassan
*fati Muhammad
*fati baffa
*maryam yahaya
*umar m shareef
*shareef Momo
*hadiza Muhammad
*Lawan Ahmed
*rukayya dawayya
*marigayi s nuhu
*marigayi ibro
Dadai sauransu
Karanta CIKAKKEN TARIHIN DADDY HIKIMA
IYALAN ALI NUHU
Ali Nuhu yanada mata Maimuna Garba Abdulkadir da yara uku Fatima da Ahmad.
Jarumin yafito da yarannasa cikin shiri mai suna zuri’a dagananne baikara sako yarsa Fatima ba saide dannasa namiji Ahmad wadda yacigaba dayin shirin ciki akwai Almajiri, Dan Baiwa, Ahmad Bin Ali Dasauransu.
KYAUTAR GIRMAMAWA
A shekarar 2005 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa (Best actor).
A shekarar 2007 ya lashe kyautar karramawa ta wadda yafi kowa cikin sabbin jarumai masu tasowa ( best upcoming actor) daga 3rd africa movie academy award.
A shekarar 2008 ya lashe gasar jarumi dayafi kowanne (Best actor) daga The future Award.
Ashekarar 2011 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa (Best actor) daga Zulu African film academy award.
Ashekarar 2012 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa ( Best actor Hausa) daga Nollywood awards.
Ashekarar 2013 ya shiga jerin wadanda suka cancanci kyautar karramawa ta “jarumi mai tallafawa jarumai” (Best supporting actor) daga 9th African movie academy awards.
Ashekarar 2013 ya lashe kyautar karramawa ta “Jarumi dayafi kowa” ( Best actor ) daga Nigeria Entertainment Awards.
Ashekarar 2013 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa (best actor Hausa) daga Best of Nollywood awards.
Ashekarar 2013 ya lashe kyautar karramawa ta “Fuskan kannywood” (Kannywood Face) daga city people entertainment awards.
Ashekarar 2014 ya lashe kyautar karramawa ta “Jarumi dayafi kowa” ( best actor) daga Kannywood awards.
Ashekarar 2014 ya lashe kyautar karramawa ta ” fitaccen jarumi” daga leadership awards.
A shekarar 2014 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa daga city people entertainment awards.
Ashekarar 2014 ya lashe kyautar karramawa ta “dogaron Kannywood” daga arewa music and movie awards.
A shekarar 2015 ya lashe kyautar karramawa ta ” jarumi da baida tsara” daga 19th African film award.
Ashekarar 2015 Jarumi dayafi kowa ( Best actor Hausa) daga Best of Nollywood awards.
Ashekarar 2015 ya lashe kyautar karramawa ta “jarumi dayafi kowa” daga Kannywood awards.
Ashekarar 2015 ya lashe kyautar karramawa ta ” Alkiblan kannywood ” daga Kannywood awards.
Ashekarar 2016 ya lashe kyautar karramawa ta jarumi dayafi kowa ( Best actor Hausa) daga best of Nollywood awards.
Ashekarar 2016 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa daga arewa music and movie awards.
Ashekarar 2016 yashiga jerin jarumai dasuka cancanci ” jarumai dasuka fi kowa” daga Kannywood awards.
Ashekarar 2016 ya sake damu shiga cikin jerin wadanda suka cancanci ” Fuskar Kannywood) daga city people entertainment awards.
Ashekarar 2016 ya lashe kyautar karramawa ta ” Karramawar Nishadi” daga arewa creative industry awards.
Shekarar 2016 ya lashe kyautar karramawa ta ” kwararren Dan wasa” daga Wazobia Creative industry.
A shekarar 2017 jarumin yayi nasarar lashe kautar karramawa ta Gwarzon Jarumi Daga Northern Nigerian peace awards.
Ashekarar 2017 yasake lashe kautar karramawa ta fuskar kannywood daga city entertainment awards.
Yasake shiga jerin wadanda suka cancanci Kyautar karramawa ta Gwarzon Jarumi Daga city entertainment awards a shekarar 2017.
A 2019 city people entertainment awards ta karramashi a matsayin Gwarzon Mai bada umarni.
Domin Karin bayani dangane da cikakken tarihin ali nuhu a YouTube Nw Hausa Tv