Cikkaken Tarihin Umma Shehu
Suna: Umma Shehu
Kwarewa: Jaruma, Maishirya fim
Fara fim: 2015
Inkiya: Zuli
Iyali: 2
Gari: Kaduna
Kasa: Nigeria
WACECE UMMA SHEHU
Umma Shehu jarumace a Nigeria, cikin masana’antar shirya Fina finan Hausa na Kannywood.
Jarumar tadade tana taka rawa cikin masana’antar sannan tana daga cikin jarumai mata wadanda suka Dade Kuma suka bada gudumawa wajen ganin masana’antar tahabaka.
Mutane dadama sun santane da suna Zuli, sunanda tasamo a Shirinnan Mai dogon zango Mai suna ‘Gidan Badamasi’
Izuwa yanzu umma shehu yafito a fim samada Hanson 50. Sannan Tasha karbar kyaututtukan karramawa dadama ciki hadda Gwarzuwar jaruma (Best actress).
Karanta: CIKAKKEN TARIHIN FATIMA HAMZA PA IZZARSO
HAIHUWARTA
An haifeta a Jahar kaduna sannan tayi karunta na matakin primary da makaranatar gaba da primary duk a Jahar kafin daga bisani tafara harkar fim.
SHIGOWARTA MASANA’ANTAR KANNYWOOD
Jaruma umma shehu ta shigo masana’antar Kannywood ne ta hanyar Jaruminnan Kuma Mai shirya Fina Finan Hausa Tijjani Asase Wadda ayanzu anfi saninsa da Kanabaro a Shiri mai dogon zango Mai suna A duniya kokuma Adahama a shirin Labarina.
Acewar Umma shehu Tijjani Asase yakasance Aminin tane Wadda take matukar darajashi tamkar Dan uwanta.
Jarumi Tijjani Asase shine Wadda yayi silar shigarta masana’antar fim inda ya gabatar da ita wa Abokinsa jarumi Adam A Zango.
DAUKAKA
Umma tafara fim ne a Shekarar 2015, a fim mai suna ‘Sa’in Sa’ Shirin data fito tareda jarumin nan, Mai shirya shiri, mawaki kuma Mai bada Umarni Adam A Zango.
Jaruma umma shehu tashigo masana’antar Kannywood da kafar dama domin da Shirin ta na fari wato Sa’in sa tasamu karramawar Gwarzuwar Jaruma na Shekarar.
Ganin kwarewar Jarumar fagen aikitane yasa masu shirya shiri dadama suka bata damar shiga shirinsu Wadda kawo yanzu tayi fim sama da 40 a masana’antar.
Karanta: Cikakken Tarihin ogah Abdul
JERIN FINA FINANTA
Jerin fina finanta suna hadada
Sa’in da
Hawan dare
Gidan badamsi shiri Mai dogon zango
Amaryar kauye
Burin masoyi
Lamba
Wuff shiri Mai dogon zango
HADAKA
Kasancewarta Jarumar data dauki shekaru a masana’antar Kannywood umma shehu tayi hadaka da jarumai dadama cikin masana’antar Wadda suka hadada:
Adam a Zango
Falalu A Daurayi
Lawan Ahmad
Ali Nuhu
Abdul m Shariff
Lilin Baba
Ummi rahab
Tijjani Asese
Dasauransu
IYALI
Umma shehu tatabayin Aure kafin shigowarta masana’antar Kannywood har tanada yara biyu.
Domin Karin bayani dangane da Cikkaken Tarihin Umma Shehu ko Kuma wasu jaruman kuziyarci YouTube namu NwHausa TV.