Cikakken Tarihin ogah Abdul

Cikakken Tarihin ogah Abdul

Suna: Abdullahi mansoor

Inkiya: Ogah Abdul

Aiki: Waka

GARI: Jigawa

Kasa: Nigeria

Cikakken Tarihin ogah Abdul
Adama A Zango tareda Ogah Abdul

Wanene Ogah Abdul

Cikakken sunansa Abdullahi Mansoor Amma anfi saninsa da Ogah Abdul Yakasance sanannen mawaki, Kuma Mai Rikodin waka daga Arewacin Nigeria.

Haihuwarsa

An haifi mawaki oga Abdul ne a ranar sha-biyu ga watan yuni a Shekara ta dubu biyu (12 June 2000) a unguwar Gujungu dake jihar Jigawa a Arewacin kasar Nigeria.

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN MUSA MAISANA A

Karatu

Ya yi karatunsa na firamare da sakandare a Gujungu, jihar jigawa, Najeriya. Yanzu haka yana karatu a jami’ar kimiya ta kano wudil jihar kano.

Farawarsa

Oga Abdul yafarane tin Yana da kananun shekaru inda yasaki wani vidiyo yana zaune a daki yana rera waka, hakan yabawa yaja hankalin Fitaccen mawakinnan Kuma jarumi Adam a Zango Wadda daga nanne yadauko Izuwa kaduna domin taimakamasa.

Oga Abdull na daya daga cikin Tauraron Mawakan Arewa da ya kamata mu sa ido a bana.

Cikakken Tarihin ogah Abdul
Ogah Abdul tareda Mahaifiyarsa

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN UMAR M SHAREEF

Mawakin Wadda ya kwarene a salon ingausa yayi wakoki masu matukar Jan hankali tin daga Shekarar 2020 zuwa 2022 Wadda kusan dukkan manyan jaruman Kannywood dakuma taurari a arewa sun hau wakar.

Daukakarsa

Mawakin yasamu karbuwa da Kuma tarun magoya baya tun bayan sake wakarsa ta Yan sa’ido dayayi a shekarar dubu-biyu da Shirin.

Saide tun daga lokacin da yasaki wakarsa ta Baza tazamana wakarsa wacce tafi fice Kuma Daya daga cikin wakokin Hausa da suka samu karbuya a wajen al’umma.

Wakarsa ta Baza tayi matukar farin jini ganin yadda Manyan jarumai da mawakan Kannywood ke hawa video challenge na wakar.

Jerin wakokinsa sun hadada

Yan sa’ido 2021
Baza 2021
Akwai batu Episode 1, 2 and 3
Azumin Bana 2022
Dasauransu

Ogah Abdul Yana daga cikin taurarin arewacin Nigeria wadanda suka halacci taro arewa turn up, taron da aka shirya musammman domin tallata jarumai, mawaka, da duk wani tauraron Hausa.

Domin Karin bayani dangane da Cikakken Tarihin ogah Abdul kokuma wasu jaruman kuziyarci YouTube channel dinmu NwHausa TV.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *