Cikakken tarihin Maryam malika
SUNA: Maryam Muhammad
INKIYA: Maryam, malika
GARi: Kaduna
KASA: Nigeria
AIKI: Jarumar film
MATAKIN KARATU: Secondary
SHAKARU:
AURE: Babu
YARA: Uku
WACECE MARYAM MALIKA
Shahararriyar jaruma kuma ficecciya a masana,antar shirya fina-finan hausa na kannywood maryam Muhammad wadda akafi sani da maryam malika
Takasance mai saukin kai da karrama mutane
KARATU
Jarumar tayi karatunta na matakin primary hadi da secondary duk a jahar kaduna saidai haryanzu bata samu damar cigaba da karatuba izuwa matakin gaba da secondary
Karanta Cikakken Tarihin Nazifi Asnanic
FARA FIM
Sannan jarumar ta fara fitowa a fim a shekarar alib dubu biyu da goma 2010 ne wani fim mesuna
_Wasila
Amma daukakarta ta farane a wani shiri mesuna
_soyayyar Facebook
Sannan ta samu damar shiga masana,antar kannywood ne ta hanun jarumi Ali nuhu
Wadda akewa lakabi da king of kannywood
Kuma ta fara harkar fimne domin ganin cewa ta samu damar fadakarwa kamardai sauran jarumai
JERIN FINA-FINAI
-Malika
-soyayyar facebook
-kona gari
-adon gari
-nagani inaso
-wasila
-wata kawa
-Wata uku -bakar kawa
-da ace bazuciya (shiri me dogon zango) series film
HADAKA
Kana jarumar tafito a Fina-finai da dama tare da jarumai da dama kamarsu
*Jarumi Ali nuhu
*Jarumi Adam A zango
*Jarumi abdul m shareef
*Jaruma nafisat abdullahi
*Jaruma jamila nagudu
Sannan manyan kawayenta a masana,antar kannywood sunhada da
*fati Shu,uma
*bilkisu shema
AURE
Jarumar ta taba yin aure amma bayan wani lokaci mai sawo auren ya rabu ta kuma sake dawowa shirin fim
Saidai haryanzu bata baiyana dalilin mutuwar auren nataba
Sannan tanada yara uku mata biyu namiji daya
KARIN BAYANI
Sannan kamar yadda ta zayyana jarumar batada wani buri kamar taga tasamu miji tayi aure
Sannan tana mutukar son turare
Kuma abincin da tafiso shine shinkafa da wake damai da yaji
A nama kuma tafison kifi
Sannan kamar yadda jama,a suke mata kallon mai saurin ido jarumar tace a zahiri sam bahaka takeba
Karanta Cikakken Tarihin Aminu Shariff Momo Northernwiki
Kana babbabn abinda yafi birgeta shine taganta a cikin yan,uwanta suna raha
Ku ziyarcemu a YouTube NW HAUSA TV domin samun karin bayani dangane da cikakken tarihin maryam malika