Cikakken Tarihin Khadija Yobe ( Karima izzarso)

cikakken tarihin Khadija yobe

SUNA: Khadija Alhaji shehu

INKIYA: khadija Yobe, Karima izzarso

SHEKARU: 1995

AIKI: jaruma

AURE: babu

MATAKIN KARATU: HND

GARI: yobe

KASA: Nigeria

cikakken tarihin Khadija yobe

WACECE KHADIJA YOBE

Khadija Alhaji shehu wacce akafi Sani da Khadija yobe shahararriyar matashiyar jaruma a masana’antar shirya fina-finai na kannywood, wacce ta yi ficce a masana,antar musamman a fim mai dogon zango na izzar so wadda ake haskawa a manhajar YouTube.

HAIHUWA

Anhaifi jarumar ne a shekarar 1995 a garin Maiduguri amma iyayenta sun kasance fulanin damaturu babban birnin jahar yobe a Nigeria.

karanta: CIKAKKEN TARIHIN AMAL UMAR

KARATU

Sannan jarumar tayi
Karatunta na primary a garin Maiduguri na jihar borno takuma yi kartunta na secondary a garin damaturu yobe state sannan ta yi HND a fannin public administration a makaranatar federal polytechnic damaturu.

FARA FIM

Khadija Yobe ta fara fim ne a shekarar 2018 sannan tafara fim ne ta dalilin zuwanta hijra wadda sukayi ta dalilin boko haram hakan yasa tayi amfani da damarta wajen yin register a masana,antar ta kannywood Kana fim nata na farko shine Wutar kara.

DAUKAKARTA

Sannan ta fara samun daukaka ne tun bayan bayyanarta a izzar-so fim mai dokon zango (series film) wadda tafito tare da jarumi lawan ahmed da ali nuhu.

JERIN FINA-FINAI

Jarumar tasha fitowa a finafinai da dama kamarsu adon gari, -hikima, -wutar Kara da sauransu

Sannan tafito acikin fina-finai masu dogon zango da dama kamarsu
izzar-so
gagare
tsaron tsaro
direba makaho muje zuwa
alajabi
bugun zuciyar masoya
sohon soja
ita nake so
zuciya daya
A T M
Da dai sauransu

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN LAWAN AHMED

KARIN BAYANI

 

cikakken tarihin Khadija yobe
Khadija yobe

Kamar yadda jarumar tazayyana iyayenta sunyi matukar yin farin ciki da fara fim nata

Kana jarumar tana daga cikin jaruman da suka shiga masana,antar ta kannywood da kafar dama duba da yadda ta samu daukaka lokaci daya

Sannan wasu masu hasashen dake hangen lamarinta jarumar khadija yobe takan iya zuwa ta wuce da dama a masana,antar
Duba da yadda ta shigo masana,antar da ilminta saboda komai da tayi sai taduba da mahangar ilmi wadda hausawa ke cewa jigon rayuwa

Sannan tana samun kwarin guywa daga wajaje da dama kamar yan jaharta yobe state da yan uwanta najini mazauna garin kano harma da maiduguri hadi da masoyanta da abokan arziki

Domin samun Karin bayani dangane da cikakken tarihin Khadija yobe Daku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube mesuna NW HAUSA TV

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *