Cikakken tarihin isah feroskhan Presidor

Cikakken tarihin isah feroskhan Presidor

SUNA: Isah Adam

Sponsored Links

INKIYA: Isah feroskhan, presdor a labarina

SHEKARU: 1985 (shekaru 36)

AIKI: Jarumi, producer

MATAKIN KARATU: Diploma

JIHA: Borno

KASA: Nigeria

Cikakken tarihin isah feroskhan Presidor
Isah feroz khan

WANENE ISAH FEROSKHAN

Cikakken sunansa Isah adam amma anfi saninsa da isah feroskhan ko kuma presidor sunanda yasamu a shiri mai dogon zango labarina wadda ake haskawa a tashar arewa 24.

Kana Yakasance shahararren jarumi a masana,antar shirya fina finan hausa na kannywood Sannan yakasance na hannun daman Adam a zango.

KARANTA: Cikakken Tarihin Aminu Shariff Momo Northernwiki

HAIHUWARSA

Jarumi isah adam haifaffen garin maiduguri ne an haifeshi a karamar hukumar monguno a jihar borno a shekarar alib 1985 amma ya girmane a jihar kano kasancewar mahaifinsa dan jihar kano hakan yasa bayan wani lokaci suka koma kanon da zama.

KARATUNSA

Saidai duk da jarumin yakasance haifaffen jihar borno ne amma ya girmane a jihar kano kuma yayi karatunsa na matakin primary da matakin gaba da primary wato secondary duk a jihar kano

Sannan yayi karatunsa na matakin gaba da secondary wato diploma a poly kano dake jihar.

FARA FIM

Sanna jarumin ya fara fitowa a fina finan hausa ne a shekarar dubu biyu da sha biyu 2012, Sannan jarumi abbas sadiq ne wadda ya fara sakashi a fim

kamar yadda ya zayyana jarumin kafin ya fara fim yakasance dan rawa wadda ke fito a bayan jarumai

JERIN FINA FINAI

_Ashabul kahfi
_Habib
_Ruwa a jallo
_Basaja gidan yari
_Sokaci

-Burin raina shiri mai dogon zango
-Labrina shiri mai dogon zango
-Sanda shiri Mai dogon zango
Dadai sauransu

Cikakken tarihin isah feroskhan Presidor
Presidor

KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN ADAM A ZANGO

HADAKA

Sannan ya fito tare da jarumai da dama a fina finai da dama
Kamarsu
*Jarumi Adam a zango
*Jarumi Ali nuhu
*Jarumi Nuhu abdullahi
*Jarumi Sadiq Sani Sadiq
*Jaruma Nafisa abdullahi
*Jaruma Halima atete
*Jaruma Maryam waziri
*Jarumi Daddy hikima
*Jarumi Al’amin buhari

KARIN BAYANI

Acewarsa Jarumi Adam A zango shine megidansa a masana,antar ta kannywood

Sannan Adam a zango yakasance shine wadda yake bashi shawara a harkar fim

Kuma shine wadda ya hanashi yin rawa saboda ganin cewa yawuce wannan matsayin yakuma yimasa alkawarin sashi a duk wani fim da yake da damar sashi

Zaku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube mesuna NW HAUSA TV dangane da cikakken tarihin isah feroskhan presidor

 

Kuyi SUBSCRIBE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *