Cikakken Tarihin Nazifi Asnanic

Cikakken tarihin nazifi asnanic

SUNA: Nazifi abdulsalam yusuf

INKIYA: nazifi asnanic

AIKI: Mawaki, darakta, furodusa

SHEKARU: 2 February 1982

MATA: Daya

YARA: Uku

GARI: Kano

KASA: Nigeria

 

Cikakken tarihin nazifi asnanic
Mawaki nazifi Asnanic

WANENE NAZIFI ASNANIC

Nazifi abdulsalam yusuf Wanda aka fi sani da nazifi asnanic mawaki ne, marubucin waka, darakta, kuma furodusa ne a masana’antar kannywood wadda yana daga cikin mawaka dasuka Dade suna bada gudumawa a masana’anatar ta shirya fina finan hausa.

HAIHUWARSA

An haife shi a ranar 2 ga watan fabrairu shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da biyu 1982, cikin jihar kano sannan mawakin yayi karatunsa na primary dakuma secondary cikin garin kano

KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN AMAL UMAR

IYALI

Kana mawakin nazifi abdulsalam Yusuf Wadda akafisani da asnanic ya kasance yana da Mata daya da yara uku, data cikinsu Maza biyu 2 da mace Daya 1.

FARA WAKA

Mawaki asnanic ya fara harkar waka ne a farkon shekarar alif 2000. Mawakin wadda masoyansa ke kiransa da mai muryar zinari yafara sake faifayin album din wakarsa ne A shekarar alif 2002, me dauke da wakoki 10 ciki har da dawo dawo da sai watarana

Baya ga kida da waka, nazifi yana daga cikin masu shirya fim dakuma bada umarnin finafinai cikin masana’antar.
Mawakin yakasance shine yayi film din rai da buri, shu’uma dasauransu.

Wakarsa tafari itace wakar fim din fil’Azal wadda mawakin ya kira wakar da bakandamiyarsa sabida itace tasa yasanu cikin masana’antar kannywood.

Mawakin ya dauki hankalin daractoti, da furodusosi ciki harda Ali nuhu da Aminu saira inda ya yi musu wakoki ga kamfanin shirya finafine na FKD dakuma Saira movie

KUDIN WAKOKI (ALBUM)

Albums dinsa sun hadada
Labarina,(2009) daga ni sai ke (2010) bunjuma (2011) Dan marayan zaki (2012) dakin amrya(2013) rauwa(2014) kambu ruwan Zuma(2013)

 

Cikakken tarihin nazifi asnanic
Nazifi

JERIN FINA-FINAI

Kana nazifi asnanic yashirya fina-finai da dama kasancewarsa furodusa amasana,antar ta kannywood
Kamar su
-almajira 2008
-jamila da jamilu 2009
-ga duhu ga haske, Mata da miji 2010
-rai da buri, muradi 2011
-dare daya, dan marayan zaki 2012
-lamiraj, shu’uma 2013
-makauniyar hanya
-kallo daya
-miyetti Allah
-gaba da gabanta
Da dai sauransu

KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN HAMISU BREAKER

KYAUTAR GIRMAMAWA

Sannan mawakin nazifi asnanic ya samu kyautukan girmamawa da dama a kasancewarsa mawaki
Kamarsu

1. Best musician 2014
(City people entertainment award)
Da dai sauransu

Daku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube domin samun Karin bayani dangane da cikakken tarihin nazifi asnanic a shafinmu mesuna NW HAUSA TV

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *