Cikakken tarihin hauwa waraka
SUNA: Hauwa abubakar
INKIYA: hauwa waraka
AURE: Babu
YARA: Babu
AIKI: Jarumar fim, yar kasuwa
MATAKIN KARATU: secondary
GARI: jos/plateau
KASA: Nigeria
WACECE HAUWA WARAKA
Shahararriyar jarumar fina finan kannywood kuma yar kasuwa hauwa Abubakar wadda akafi Sani da hauwa waraka takasance jaruma kannywood mai hazaka da cika alkawari saidai wasu suna mata ganin mace marar kunya wadda kuma a zahiri ta zayyana cewa ba haka takeba
HAIHUWA
Anhaifi jarumar ne hauwa abubakar a garin jos
Sannan ta girma a jahar kano kafin daga bisani ta kara komawa garin jos da zama wadda har ya kai ga tayi aure a chan
Sannan ta kara dawowa jahar kanon da zama bayan aurenta ya mutu wadda hakannema yayi sanadiyyar fara fitowarta a masana’antar shirya fina finan hausa na kannywood saidai jarumar bata bayya shekarar da tafara fitowa a fim ba
Karanta CIKAKKEN TARIHIN FATIMA HAMZA PA IZZARSO
KARATU
Sannan jarumar tayi karatunta na primary hadi da matakin gaba da primary wato secondary duk a jahar kano saidai haryanzu bata samu damar cigaba da karatunba.
FARA FIM
Sannan jarumar kamar yadda ta zayyana ta fara fitowa a fimne kawai bisa ra’ayin kanta
Sannan duk da cewa bata da uban gida a masana’antar bata fuskanci wani kalu baleba kafin farawarta kamar dai sauran jarumai
DAUKAKARTA
Sannan jarumar hauwa Abubakar wadda akafi sani da hauwa waraka takasance a masana’antar kannywood na sawon lokaci amma daukakarta ya farane tun bayan fitowarta a wani shiri mai suna
_waraka wadda anannema ta samo sunan waraka, da kuma
_Katanga wadda shima ya bada gudun maw a
Wajen sanuwanta, da
_fati yar adamawa
JERIN FINA FINAI
Sannan tafito a fina finai da dama kamasu
_Alkalin kauye
_fati yar adamawa
_waraka
_katanga
_kayi nayi
Dadai sauransu
Sannan tana daga cikin jaruman cikin shirin _gidan badamasi fim mai dogon zango wadda ake haskawa a tashar Arewa24
HADAKA
Sannan jarumar tafito a fina finai da dama tare da jarumai da dama kamarsu
*Ali nuhu
*Adam a zango
*Falalu a dorayi
*Tijjani asase
*Jamila umar nagudu
*Hadiza gabon
*abba almustapha
Dadai sauransu
Karanta CIKAKKEN TARIHIN ALI NUHU
KYAUTAR KARRAMAWA
Sannan ta karbi kyautukan girmamawa da dama a ciki da wajen kasar a fina finanta da dama kamarsu
-kannywood movie award
-African movie
-Nigerian upcoming actress award
Dadai sauransu
KARIN BAYANI
Sannan kamar yadda ta zayyana batada mai gida a masana’antar kannywood
Sannan ta taba aure amma bata haihuba
Sannan babban burinta shine taga tayi aure
Sannan daku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube NW HAUSA TV domin samun karin bayani dangane da cikakken tarihin hauwa waraka