Tarihin Safiya Yusuf ( Safara’u kwana casa’in Biography)

Tarihin Safiya Yusuf ( Safara’u kwana casa’in Biography)

Cikakken suna: Safiya Yusuf

Inkiya: Safara’u, Safara’u kwana casa’in
Kwarewa: Jaruma, Waka
Aure: Babu
Gari: Kano, Ibadan
Kasa: Nigeria

Cikakken sunanta Safiya Yusuf Amma anfi sanita da Safara'u, Sunanda tasamo shi a shiri Mai dogon zango Wadda arewa24 ke shiryawa Mai suna kwana casa'in.
Safeeya Yusuf Safara’u kwana casa’in

WACECE SAFIYA Yusuf

Cikakken sunanta Safiya Yusuf Amma anfi sanita da Safara’u, Sunanda tasamo shi a shiri Mai dogon zango Wadda arewa24 ke shiryawa Mai suna kwana casa’in.

Takasance jarumace, Kuma mawakiya wacce tayi suna lokaci guda duba da yanayin kyanta dakuma rawarda tataka a masana’antar.

Karanta: Tarihin Feezy YNS ( Feezy Biography)

Haihuwarta

Anhaifi Jaruma Safara’u ne a cikin garin Kano saide kasancewar mahaifinta yasamu canjin wajen Aiki Izuwa ibadan Dake kudancin Nigeria hakan yasa suka koma can inda tayi karatunta na matakin nursery dakuma primary.

Daga bisani mahaifinta yasake samun sauyin wajen Aiki Izuwa garin Kano hakan yasa suka sake dawowa Gida takuma cigaba da karatunta daga matakin junior secondary School Izuwa senior secondary School.

Daukaka

Jaruma safeeya Yusuf tafara fitowane a Shirin kwwana casa’in Wadda shine silar daukakarta har yazuwa fara fitowa a wasu shirye shirye masu dogon zango dama na masana’antar Kannywood.

Jarumar tafito a wani shirna masana’antar Kannywood Mai suna Direba makaho tareda jarumai irinsu Ado isah gwanja, ayatullahi tage, sulaiman bosho, Alhassan kwale dasauransu, Wadda mai shirya Fina finai kwakwatawa ya shirya.

Tarihin Safiya Yusuf ( Safara'u kwana casa'in Biography)

Fita daga kwana casa’in

A shekarar dubu biyu da Shirin da biyu ne Jarumar tafita daga cikin Shirin kwana casa’in sabida cin dunduniyarta da akayi aka yada wani videonta ga duniya.

Karanta: Rikima tsakanin Nafeesat Abdullahi da naziru sarkin waka

Fara Waka

Tin bayan ficewar Jarumar a shekarar dubu biyu da ashirin bata karayin wani Abu Wanda yadau hankalin al’ummar Hausawa ba.

Sai a shekarar 2022 tin bayan hadewarta da mawakin nan Mai suna 442 (mr442).

Safiya Yusuf (Safara’u) Tareda 442 sun saki wata Waka Mai suna “KWALELENKA” a shekarar 2022.

Wakar tajawo maganganu dadama masu Dadi dama marasa Dadi wajen al’ummar Hausa.

Domin Karin bayani dangane da Tarihin Safiya Yusuf ( Safara’u kwana casa’in Biography) kokuma wasu jaruman kuziyarci YouTube channel namu a New Hausa TV

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *